Me Harin ‘Yan Bindiga Kwalejin Horas Da Hafsoshin Soja (NDA) Ke Nufi Ga Tsaron Kasar Nan?

Hafsoshin Soja

Daga Khalid Idris Doya, Abuja

A tsakar daren ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga dadi da har zuwa yanzu ba san ko su waye ba suka kutsa kai cikin Kwalejin Sojoji da ke Kaduna wato (Defence Academy, NDA), inda suka kashe hafsoshin sojoji biyu tare da yin garkuwa da soja mai mukamin Manjo.

Wannan lamarin ya yi matukar tada hankalin al’umman Nijeriya ganin yadda lamarin ya zo musu sabo, musamman ma ba a cika jin labaran da ke cewa ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane na iya karfin halin shiga barikoki domin kai hari ba, sannan kuma in aka yi nazarin girman NDA a matakin tsaro hakan ma na iya kara jefa jama’a cikin dardar.

Sai dai hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa lallai kawo yanzu sun tashi tsaye domin kamo maharan don su dandani kudarsu, kuma sun bada tabbacin cewa a kwantar da hankali domin suna kan bincike a halin yanzu.

Kan wannan lamarin, LEADERSHIP HAUSA ta tuntubi masana tsaro don jin ra’ayinsu kan wannan lamarin inda suka haska lamarin tare da nusar da hukumomin matakan da ya dace a dauka domin dakile faruwar hakan gaba cikin wannan rahoton na musamman da muka hada.

Manjo Abdullahi Adamu Kwazo Zuru (Ritaya), masani ne kan tsaro kuma tsohon jami’in soja da ke sharhi kan lamarin tsaron kasa, ya nuna cewa tabbas akwai inda aka yi ba daidai ba, yana mai cewa muddin ‘yan bindiga za su iya kusa kai cikin Kwalejin Tsaro ta kasa (NDA) to kuwa babu wani wurin da ke da tsaron da ba za su shiga ba a Nijeriya.

A cewar Manjo Kwarzo: “Abin da wannan hatsarin na Kwalejin tsaro ya nuna mini kuma hangena ya bani shi ne babu inda yake da tsaro a kasar nan, ko’ina ba lafiya yake ba. Idan har za a iya shiga cikin NDA a yi irin wannan ta’asar to babu inda ba za a iya shiga a yi irin wannan ta’asar ba; domin ni in ka barni zan iya cewa har fadar shugaban kasa za a iya shiga ke nan. In dai har za a iya samun damar kutsawa cikin NDA a yi abun da aka yi, abun babu dadi sam.

“Dole ne sai a koma ‘Drawing Board’ mu ga mene ne aka yi ba daidai ba a yi gyara. Domin idan ka je NDA za ka ga ta waje-waje da wasu muhimman wurare duk akwai na’urorin daukan hoto (CCT Camera) kusan ko’ina kake ana iya ganinka. To ta yaya za a ce an shiga wajen nan ba tare da an ga wadanda suka shiga ba? Kuma idan an koma cikin na’urar daukan hoton ai suna nadan abubuwan da aka yi da ababen da suka faru, a je a kunna a yi tariya domin a ga abubuwan da suka faru daga farko har karshe.

“Bai kamata a ce ba a san wadannan mutanen da suka shiga suka kai harin nan ba, ya kamata a san ko su waye. Kuma tsakani da Allah in har an shiga cikin NDA an yi wannan aika-aikar to babu inda ba za a iya shiga ba.,” inji shi.

Manjo Kwazo ya kara da cewa, sakacin da ya jawo wannan matsalar na tsaro ya shafi bangaren hukumomi da kuma shugabanin tsaro, yana mai cewa matakin gyara dole sai an cire son kai da son zuciya domin a yi aikin da zai dawo da martabar tsaron kasa.

“Mu tsaya mu yi wa kanmu magana tsakani da Allah ko fannin daukan aikin soja da dan sanda kawai ya ake yinsa a halin yanzu? Akan dauki wadanda suke son yin aikin ne ko kawai ana daukan masu galihu ‘yan alfarma ne? Ni lokacin da na je NDA ban san kowa ba aka min tambayoyi aka tantance daga baya aka ce an dauke ni Janar Sani Abacha (Allah mishi Rahama) shi ne shugaban zaban wadanda za a dauka a lokacin, muna nan ya zo ya ce mana da wane-da-wane an zabeku an daukeku ku dawo ranar kaza domin ku ci gaba da yin ‘training’ horo. Amma yanzu mu je mu duba haka ake yi?

“Sai fa an duba daga tushe a ga wai inane aka yi kure aka yi ba daidai ba, in ba a san abun da yake ba daidai ba, ka dauki abun da yake fari ka sa baki ka dauki inda baki yake ka kaisa wurin jaa abun nan ba zai iyu ba; dole ne sai an koma an yi gyara tsakani da Allah. Duk lokacin da za a dauki sabbin jami’ai a fitar da sanarwar ta gaskiya masu sha’awar aikin a dauke su.”

Yana mai cewa, muddin idan aka koma daukan aiki tun daga tushe na wadanda suke son aikin soji ko dan sanda tsakani da Allah za a samu bakin zaren rage matsalolin, yana mai cewa duk mai sha’awar aikin zai yi kokarin kare kasa da ‘yan kasa iya kokarinsa.

“Ya kamata a gyara tsarin biyan hakkoki, duk jami’in da ya rasa ransa bai dace a dade ba a biya iyalansa hakkinsa ba, rashin hakan yana sanyaya guiwa ya hana wani zage damtse wajen tunkarar matsalar tsaro domin gudun halin da iyalansa za su shiga bayan baya nan.

“Na karanta wani rubutu da ke cewa kila wadanda suka yi wannan ta’asar wadanda suka taba aikin NDA ne da aka kora, ka ga idan an kori ma’aikaci akwai hakkin da ya kamata a biya shi, shi wannan kudin in an baiwa mutum mai dan tsoka zai ba shi damar samun aikin da zai yi (sana’a) da ba zan sanya ya yi tunanin wani aika-aika ba; ka ga ko irin wannan ya dace gwamnati ta duba, duk wani mai hakki ake biyansa a kan lokaci.”

Dakta Adamu Ahmad, malami a tsangayar koyar da ilimin sanin halayyar dan adam (Sociology) a jami’ar jihar Gombe, ya shaida wa jaridar nan cewa, tun da farko har zuwa yanzu, gwamnatoci da jami’an tsaro ba su dauko hanyoyin dakile matsalar tsaro ba ne, ya na mai cewar babbar matsalar tsaro a kasar nan a halin yanzu shine babu wani abu guda da ‘yan ta’addan ke amfani da shi da aka iya toshewa ko aka shawo kansa, don haka ne yake mai cewa muddin ana son kawo karshen matsalar kuwa dole sai an tashi tsaye an toshe inda suke samun makamai, masu samar musu da bayanan sirri da kuma toshe inda suke samun sabbin mambobi kafin a fara tunanin maida matsalar tsaro zuwa tarihi a Nijeriya.

Dakta Adamu Ahmad na cewa: “Kusan a wurare daban-daban da muke tattaunawa kan lamuran tsaro mun sha hasashen cewa za a iya zuwa wani lokacin da hakan zai iya faruwa, sannan wannan lamarin ya nuna gazawar jami’an tsaro da ake ganin kamar alhakin samar da tsaro tare da dakile daukan makamai ga ‘yan bindiga din ke wuyansu. Idan har wani abu makamancin wannan zai faru ya nuna maka cewa wanda baida komai (farar hula) rayuwarsa na cikin matukar hatsari.

Daktan ya cigaba da cewa, babban matsalar shine babu tsari na kawar da matsalar ma har zuwa yanzu, “kuma gaskiya kamar yadda muka sha fada tsari ne na harkokin tsaron da ke kasar babu tsari guda da za a ce ana amfani da shi domin magance matsalolin tsaro, kowace hukuma tana yin abun da take ganin za ta iya yi ne a lokacin da bukatar hakan ya taso ko don ta dakilewa ko kuma don ta nuna tana yin aikinta ba ta zauna ba. Wannan kusan shi ne ya kara ta’azzara matsalar tsaro a Nijeriya.”

“Yanzu misali babu yadda za a yi a ce masu dauke da makami ka yi ta kokarin yakarsu, sannan a gefe guda kuma baka da tsarin da zai hanasu shigo da sabbin makamai, babu wani tsari da zai hanasu samun kudaden shiga ko tsarin da zai iya nuna wadanda suke basu bayanan sirri, babu wani bayanin sirri kuma da zai iya gurgunta abubuwan da suke yi. ba ka iya hana yadda suke yadda suke jawo wasu a jikinsu domin su kara karfa to ko shekara nawa za a yi ba za a iya kawo karshen yakin ba.

Dakta Adamu ya ce, ababen da suke akwai da suka haifar da matsalar tsaro sun hada da talauci da rashin aikin yi, sai yake mai nusar da cewa dukkanin kokarin jami’an tsaro ba za su iya shawo kan wannan matsalar na rashin aikin yi da na ilimi ba, sai yake mai nuna cewa aiki ne da ke kan gwamnatoci amma in lamarin ya juya ya zama matsalar tsaro a nan ne jami’an tsaro ke yin nasu, yana mai bada ra’ayin cewa, don meye ba za a magance matsalolin da ke ma haifar da mutane suna tsunduma kansu cikin harkokin ta’addanci ba.

Matsalar ‘yan garkuwa da mutane a Nijeriya dai ba yau ne farau ba, hatta gwamnoni sun sha ankarar da irin barazanar da Nijeriya ke ciki, domin ko a kwanakin baya ganin yadda rikicin ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa, Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya nunar da cewa lamarin ya fara hararar mamaye Nijeriya bisa yadda yake kamari.

Gwamnan Matawalle, ya bayyana cewar ‘yan bindigan da a yanzu haka ke cin karensu babu-babbaka a jihohin Arewa Maso Yammaci muddin ba a gaggaauta daukan matakan dakile su ba, to kuwa suna da karfin da za su iya mamayewa ko kutsa kai cikin illahirin shiyyar Arewacin kasar nan baki daya da ma sauran sassan Nijeriya.

Matawalle wanda ya shaida hakan a Jihar Kaduna sa’ilin da yake gabatar da wata mukala mai taken “Yaki Da ‘Yan Bindiga a Arewa Maso Yammacin Nijeriya: Kalubalen Da Ke Makale Wajen Shawo Kan Matsalolin”, a yayin taron kaddamar da sabbin kungiyar Arewa Media ‘Writers Association da ya wakana Kabir Gymnasium.’ Kwanakin baya.

 

Exit mobile version