Connect with us

Uncategorized

Me Ke Jajo Aure Da Saki Tsakanin Hausawa

Published

on

Tambayoyi ne masu saukin amsawa, amma cike suke da rudani idan ba an bi a hankali ba za a iya fadowa, ba kuma za a iya fitowa daga inda aka fadan ba. Ke nan sai an yi takatsantsan kafin a dumfari amsa irin wadannan tambayoyi.

Daga cikin tambayoyin akwai wai me ya sa ake yawan yin aure da saki a tsakanin Hausawa? Me ya sa maza ke daukar matan da suka aura tamkar rakuma da akala? Ya ya kamata su kasance dangane da biyayya ga juna da kare martabar aure da hakkokin auren? Me ya sa kullum in aure ya lalace ba a cika ba mazan laifi ba, an fi rataya komi ga mata? Shin auren Hausawa na bisa turbar addini ne ko kuwa al’adu ko kuwa gashi nane ne? Duk yadda mutum ke so ya kalli wadannan tambayoyi da idon rahama, ya kuma amsa su domin a fahimta da kawo gyara, sai ya ja dogon numfashi tukunna.

Amma ta hanyar nazarin rayuwar Hausawa jiya da yau da kuma lakantar yadda masanan baya suka dubi matsalar za a iya kokarin amsa tambayayoyin.

Idan kuma aka dubi yadda jahilci da lalaci da talauci su kama, kuma suke addabar al’ummar Hausawa/Fulani za a iya samun hasken amsa wadannan tambayoyin game da aure da saki a tsakanin Hausawa.

A natsu a kalli wadannan abubuwa da kyau, musamman a cikin harkar aure da saki a tsakanin Hausawa za mu fahimci cewa suna da hannu bisa irin harkallar abin da ke faruwa a halin yanzu. Me ya sa?

Shi dai aure a halin yanzu ga Hausawa/Fulani duk da cewa bisa turbar addinin Musulunci ake dora da gudanar da shi, amma kusan kashi 7 ciki 10 al’adu ke masa wurin zama, kama tun daga neman auren, zuwa bayarwa da shirye-shiryen auren da sauran hidindimu da kuma rayuwar zaman auren ta fuskar tanadar wurin zama da cimaka da ilmantarwa da zamantakewa baki daya. Ba kuma wani abu ya sa al’adu suka yi katutu a cikin rayuwar aure da saki ba sai saboda duhun jahilci da lalaci da ya mamaye al’ummar tamu.

Yawancin mu ba mu san me ya sa ake aure ba, wani sharudda ake bukata a cika kafin a yi auren, ko ya ya hakkokin mijin da matar suke ko kuma wace rawa waliyai da wakilai da shaidu da sauran al’umma za su iya takawa wajen hadawa da raba aure. A yawancin wadannan batutuwa da suka shafi hadi da raba aure, za a ga al’adu ne kan gaba, ba Shari’a ba, ke nan dole a yi ta kafsawa tsakanin al’umma.

A sani duk inda son rai ko jahilci suka kasance Limamai, musamman a batun gina rayuwar aure, sa’annan lalaci ya kasance Ladani, to sallar da za ta biyo ita ce ta kuncin talauci da damuwa. Aure da aka gina shi bisa Sunna da Shari’a yana bukatar abubuwa biyar manya, cikin su mai muhimmanci sosai (duk da cewa sauran suna da muhimmanci) ba irin waliyai da wakilai da shaidu. Me ya sa? Idan ana son aure ya yi karko, saki ya ragu, in an yi maganin jahilci da lalaci da talauci, sai a koma ga mahada auren da shaidu, wato ta inda aka hau, ta nan ya kamata a sauka. Yadda waliyai da wakilai suka sa hannu wajen ba da auren, ya dace su san da batun sakin da dalilin yin sa in an tashi yin sa daga ma’auratan, ta haka sai ka ga waliyai ko wakilai ko shaidu sun sa baki, an yi wa tufkar hanci, ba irin yanzu ba da wasu ke ganin ai jarunta ma ce a yi saki ko kuma sakarkaru ne kadai ke yin saki. Ba wani abu ya sa haka ba sai ganin ba mai kula da batun sakin da an yi auren, an bar miji da nuna isa a harkar aure da saki.

Mun dai riga mun san cewa aure Sunna ce muwakkada, kuma duk wanda ya yi niyyar aure bisa Sunna da Shari’a ya kamata ya san cewa akwai dokoki na zaman tare da kuma sharudda na rabuwa. Ba lasisi ba ne ga miji ya yi yadda ya ga dama da igiyar da ke hannunsa, kuma ma ai igiyar ba shi kadai ke rike da ita ba, matar na iya riko da igiyar a wani lokaci. Amma irin yadda aka dauka matar ba ta da hannu a saki, shi ke sa mazan ke zama masu karfi, su yi yadda suka ga dama, daga saki daya har zuwa dubu suna yi, don sun isa, duk da cewa ba a sunnanta haka ba; da yake kuma Shari’a ta yi karanci, sai a dauka hakan shi ne daidai.

Idan har maza sun san cewa ba haka nan ake saki barkatai ba domin Shari’a ta tanadi matakan bi don yin sakin, sannan kuma kowane saki da fansar da za a ba matan da irin abin da ke faruwa yanzu ya ragu ko ba a hana baki daya ba. Alal misali, idan maza sun san cewa saki daya ko biyu ba korar kare ake wa matan ba, zama ne a cikin gida har kammala idda wato a ba matan muhalli da ci da sha da abin da maza ke ji a ransu game da sakin mata ba kai ba hakan da bai taso ba. Idan maza sun san cewa matar da ta kammala idda, kila tana shayarwa tana da ikon ta ajiye musu ‘ya’yan ta yi gaba, ya shayar da su da kan sa, tun da hakkin shayarwar a wurin mazan yake da an sami saukin sakin mata. A tuna fa matan na da zabin mazan da suka sake su, su biya su domin shayar da ‘ya’yansu bisa tanadin Sharia’a. Haka kuma da maza sun cewa matar da aka saka ta wuce da ‘ya’ya gidan iyayenta, ba hakkinta ba ne ta rene su, hakkin na mazan ne, iyayensu; wato su ba su wurin kwana da ciyar da su da tufatar da su da kula da lafiya, har su girma da ba a samu masu gigin saki haka nan siddin matsalakan ba. Da mazan sun san cewa sakin da aka ce a yi wa mata, an so a yi shi da kyautatawa ne, ba da muzgunawa ba, da an rage wasu abubuwan da ake yi yanzu.

Duk wadannan da ma wasu irin su ana bukatar abubuwa kamar uku ko hudu domin su tabbata; wato a kawar da jahilci da lalaci da radadin talauci, a kuma tabbatar da an dabbaka Shari’a a tsakanin al’umma, domin aure da zaman auren da saki ko rabuwa Shari’ar ta tanade su ba wasu can daban ba. Amma shin ana gudanar da Shari’ar a tsakanin al’ummar?

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: