Shugaban Kungiyar Tijjaniyya na Afrika, Sheikh Mahy Ibrahim Inyass, ya sanar da tsige Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Khalifan Tijjaniyya a Nijeriya.
Wannan sanarwa na kunshe ne cikin wata takarda wacce aka rubuta kuma aka aike wa manema labarai da sauran mambobin Kungiyar Tijjaniyya da ke fadin Nijeriya a ranar Talata 26t ga watan Nuwambar, 2024.
- Yadda Sarki Sunusi Lamido Ya Yi Bikin Shiga Fadar Kano Tsakar Dare
- Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II
Takardar mai dauke da sa hannu shugaban Kungiyar Tijjaniyya na Afrika, Sheikh Mahy Sheikh Ibrahim Inyass, ta ce daga yau ta tsige Sanusi Lamido Sanusi daga Khalifancin Tijjaniyya kuma ta soke ofishin Khalifancin Tijjaniyya a Nijeriya.
Sheikh Mahy ya ce, “Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne zai ci gaba da shugabantar duk wasu harkokin Kungiyar Tijjaniyya da ke fadin Nijeriya tare da tallafawar Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Husaini”.
Sai dai kuma duk wani kokari na jin ta bakin bangaren Sanusi Lamido Sanusin ya ci tura kasancewar kowa ya rufe bakinsa. Wata majiya ta kusa masu ruwa da tsakin harkokin Tijjaniyar ta nuna cewa wannan sanarwar ba ingantacciya ba ce, musamman rashin samun takamaiman wata hujjar yin hakan. Amma dai lokaci ne zai tabbatar da wannan lamari.