Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

Me Saukar Shugabannin Tsaron Nijeriya Ke Nufi?

by Muhammad
January 27, 2021
in MANYAN LABARAI
3 min read
Shugabannin Tsaro
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
  • Sauka Suka Yi Don Kashin Kansu – Fadar Shugaban Kasa
  • Su Waye Sababbin Shugabannin Tsaron Nijeriya?

Daga Nasir S. Gwangwazo,

A jiya ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi wani namijin kokari ya amince da saukar Shugabannin Rundunonin Tsaron kasar, wadanda suka hada da Babban Hafsan Tsaro, Janar Abayomi Olonisakin; Babban Hafsan Sojojin Kasa, Tukur Yusuf Buratai, Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Marshal Sadikue Abubakar, da Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Bice Admiral Ibok Ekwe Ibas, wadanda tuntuni da ma lokacin ritayarsu daga aiki ya wuce.

samndaads

Sauke shugabanni tsaron zai iya kawo karshen cece-kuce da tereren da aka jima ana yi wa Shugaba Buhari bisa zargin sa da barinsu su cigaba da aiki duk da cewa, lokacin  ritayarsu ya yi ba tare da ganin harkokin tsaron kasar yana bunkasa a karkashinsu ba, kamar yadda masu zargin ke gani.

Sai dai kuma, sabanin yadda aka rika bayar da wasu rahotannin cewa, Shugaba Buhari ya kore su ne, Fadar Shugaban Kasar ta sanar da cewa, sune suka sauka a kashin kansu, inda Buharin shi kuma ya amince da hakan.

Sai dai kuma sanarwar ba ta tsaya iyaka nan ba, domin ta bayyana nada wasu sababbin shugabannin tsaron nan take.

Manjo Janar Lucky Eluonye Onyenuchea (LEO) Irabor shine sabon Babban Hafsan Tsaro na Kasa, shi kuma Manjo Janar Ibrahim Attahiru shine sabon Babban Hafsan Sojojin kasa, sannan Air Bice Marshal Isiaka Oladayo Amao ya zama sabon Babban Hafsan Sojojin sama, yayin da Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo ya zama Babban Hafsan Sojojin Ruwa.

Manjo Janar Irabor, wanda shine Kwamandan Horar da Sojoji dake Minna kafin nadin nasa, an haife shi a ranar 5 ga Okotoba, 1965, a Aliokpu Agbor dake yanzkin Karamar Hukumar Ika ta Kudu a Jihar Delta.

Ya samu shiga Kwalejin Horar da Kananan Hafsoshin Soja (NDA) dake Kaduna a 1983, inda kasance a Kwas na 34, kuma an rantsar da shi a matsayin Second Laftanar ne a ranar 28 ga Yuni, 1986, inda ya fara aiki a sashen aikawa da sakonni na Sojojin Kasa. Ya halarci kwasa-kwasai da dama a gida da waje kan kwarewar aikin soja kafin hawa wannan mukami a jiya. Ya kuma samu digiri na biyu a Jami’ar Ghana da Bangaledash a lokuta daban-daban, sannan ya halarci fagen dama a gurare da yawa na cikin gida da waje,

Shi kuwa sabon Babban Hafsan Sojojin Kasa, Manjo Janar Attahiru, mai lambar aikin soja ta 8406, an haife shine ranar 10 ga Agusta, 1966, a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, kuma ya shiga NDA dake Kaduna ne a Kwas na 35.

Kafin ba shi jagorancin sojojin kasan, shine Kwamandan bataliyar soja dake Inugu ta 82, inda gabanin nan ya taba rike ragamar Rundunar Lafiya Dole dake Maiduguri, wacce ke fafatawa da Boko Haram.

Sabon Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Marshal Amao, kuwa an haife shi a ranar 14 ga Satumba, 1965, a jJihar Inugu, amma iyayenssa ’yan asalin Karamar Hukumar Oshogbo dake Jihar Osun ne.

Sabon Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Rear Admiral Gambo, wanda an haife shi ranar 22 ga Afrilu, 1966, dan asalin Karamar Hukumar Nasarawa dake Jihar Kano ne. ya shiga makarantar horon aikin soja ne a ranar 24 ga Satumba, 1984 a Kwas na 36, kuma an rantsar da shi a aikin soja ne ranar 24 ga satimba, 1988.

Ya halarci kwasa-kwasai da dama na harkokin tsaro, musamman ta fuskar sufuri da jigila, kuma yana da babbar difloma ta PGD, baya ga halartar kwaa-kwasai a kwararru lokuta daban-daban.

SendShareTweetShare
Previous Post

Korar Makiyaya A Ondo: Cikakken Rahoton Yadda Ta Kaya Taron Gwamnoni Da Shugabannin Fulani

Next Post

Sabuwar Cuta Ta Kashe Mutum Hudu A Sokoto

RelatedPosts

'Yan Adaidaita

An Sasanta Yajin Aikin ’Yan Adaidaita Bayan… Motocin ‘Kano Line’  Sun Koma Jigilar Jakara-Kasuwa

by Muhammad
3 days ago
0

Babu Hanunmu A Ciki Wannan Yaji – Shugaban ’Yan Adaidaita...

Adaidaita

Yajin Aikin Adaidaita: Acaba Ta Dawo A Kano

by Muhammad
4 days ago
0

Ya Jefa Jama’a Cikin Tsaka Mai Wuya Yadda Aka Koma...

Masu Garkuwa

Tattaunawa Da Masu Garkuwa: Yadda Gwamnonin Kaduna Da Neja Suka Raba Gari

by Muhammad
5 days ago
0

Shin Sheikh Gumi Ne Ya Raba Tsakani? Daga Nasir S....

Next Post
Sabuwar Cuta Ta Kashe Mutum Hudu A Sokoto

Sabuwar Cuta Ta Kashe Mutum Hudu A Sokoto

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version