Me Ya Baiwa Kasar Sin Nasarar Dakile Cutar COVID-19 Cikin Kankanin Lokaci?

Masu hikimar magana na cewa ba’a bori da sanyin jiki, ko da yake, masana da dama a matakai daban daban sun sha bayyana ra’ayoyinsu game da abin da suke ganin su ne dalilan da suka baiwa kasar Sin cimma nasarorin da ta samu a yaki da annobar COVID-19 tun bayan barkewar cutar a farkon wannan shekara. Duba da irin managartan matakan da kasar ta dauka a karon farko domin yin kandagarki domin dakile bazuwarta cutar, matakan da suka kasance a matsayin zakaran gwajin dafi a yaki da cutar barkewar numfashin wacce aka fi sani da COVID-19. Sai dai duk da irin yadda masanan ke yin sharhi game da batun, amma akwai wani muhimmin sirri da ya kamata duniya ta lura da shi. Wannan sirri da nake kokarin fayyacewa shi ne, wata akida da mahukuntan kasar Sin suka dauka mai taken “mayar da lafiya da tsaron jama’a a gaban komai”. Wannan batu da nake kokarin bayyanawa za mu iya cewa faduwa ce ta zo daidai da zama, kamar yadda mataimakin sakataren jam’iyyar NRM mai mulkin kasar Uganda Richard Todwong da takwaransa shugaban matasa na jam’iyyar Augustine Otuko, sun bayyana cewa, duniya na bukatar koyi da akidar kasar Sin na mayar da jama’a a gaban komai, tsarin da a cewarsu, shi ne kashin bayan ci gaban tattalin arziki da rayuwar al’ummar Sinawa da ma nasarar da kasar ta samu a yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Ko shakka babu, duk shugabannin da suka dauki akidar mayar da rayuwa da tsaron al’ummarsu a gaban komai lallai za su cimma nasarar kaiwa ga gaci a duk wani yunkurin da mahukunta suka tsara gudanarwa, kamar yadda ’yan magana ke cewa in gani a kasa wai an ce ana biki a gidan su kare. Lallai duk lokacin da al’ummar kasa suka lura cewa shugabanninsu sun maida hankali kan bukatunsu, da moriyarsu, da tsaron lafiyarsu, la hakka su ma jama’ar za su ramawa kura aniyarta, ma’ana za su yiwa hukumomin cikakkiyar biyayya domin a gudu tare a tsira tare. Wadancan jami’ai na Uganda da na ambata sun nuna cewa, fahimtar wannan tsari ne ya sa jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, JKS, take jagorantar kasar bisa turbar raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummarta. A karkashin tsarin JKS akwai tsari na tuntuba game da bukatun da suka shafi al’ummar Sinawa. Manufar haka ita ce, yin gyara ko ci gaba a wuraren da suka dace. Hakan ya sanya jama’a zama kashin bayan jam’iyyar. Ko shakka babu, ya kamata shugabanni a fadin duniya, su rungumi tsarin mayar da jama’arsu a gaban komai yayin da suke tsara manufofi, domin yin hakan yana sanya jama’a da hukumomin bayar da tasu gudunmawar wajen aiwatar da duk wata ajandar raya kasa. Gyara kayanka dai ba zai taba zama sauke mu raba ba. (Marubuci: Ahmad Fagam daga CRI Hausa)

Exit mobile version