Hamza Dawaki" />

Me Ya Fi Saukin Fuzgar Zukatanmu  Zuwa Son Mutum? (4)

Wannan shi ne mako na hudu da muke tattauna wannan batu, dangane da dalilan da suke wasa mutum ya ji yana son ko sha’awar wani. A makon da ya wuce, mun tsaya a kan wata gaba, wadda take tabbatar mana da abubuwa biyu. Wato kayatuwar da Peter da masoyiyarsa suka yi da juna, bayan gajeriyar tattaunawa. Na farko, mun fahimci cewa, ashe mutum gundarinsa shi ne ya fi tasiri, Ba fuska ko wasu sassan jiki wadanda suke kayatar da ido kawai ba. Harwayau, mun fahimci cewa ba wai iya kuranta kai ko nuna kai wani ne a gaban mace yake sawa ka samu karbuwa ba. Ana samun karbuwa ne a wurin wanda ake so kawai idan an yi wani abu da ya faranta masa, ya sa shi ya ji shi ma yana da muhimmanci.

Yanzu za mu ci gaba da bin wadannan gwagware muna kallon jujjuyawa da matsinsu a hannun masanan. Don ganin abin da zai tunkude wa Buzu rawani.

Harshenka Alkalinka.

A zagaye na farko, Baht ta zauna da wanda masanan suka yi tsammanin za su iya zama masoyan juna da shi. Kuma bisa dukkan alamu ya dan kayatar da ita. Abin mamaki, sai ga shi a zagaye na biyu, lamarin ya dau sabon salo. Domin a wannan zagayen dai bayan tattaunawarsun sai ga shi ta ba shi maki 12 kacal. Kodayake Dr. Gleen yana ganin babu abin da ya karya alkadarinsa kamar rashin iya bakinsa, yayin tattaunawar.

Bayan wannan matashin ya yi mata ‘yan tambayoyi kadan game da abin da ya shafi aiki da adireshinta, katsam sai kuma ya tambaye ta. “Shekarunki nawa?’’ Nan take kuma wasu alamomin yake suka bayyana a cikin murmushin nata. Sannan ta amsa; “Shekaruna talatin da uku.” Ya kara maimaitawa; “Talatin da uku!” Sannan suka ci gaba da tattaunawarsu. Sai dai daga kan wannan gabar wanda duk ya yi mata kallo irin na kwakwa zai iya fahimtar lallai murmushinta dan jabu ne.

Kodayake dama, yana tambayarta batun shekaru, Dr. Gleen wanda yake kallon tattaunawar tasu a cikin kwamfuyutarsa, ya tabbatar da cewa lallai ya kwafsa, domin mata sam ba sa so a tambaye su shekarunsu a irin wannan gabar. Musamman ma wadanda shekarun nasu suka dan tura, irin ta.

 

Kyalliya Ba Karya Ba Ce.

Idan za mu iya tunawa dai, tun a can baya mun bayyana cewa Baht, ita kadai ce wadda ta samu gudunmawar wata kwalliya ta musamman daga cikin matan. Wadda kuma masanan suke sa ran idan an jefa ta cikin mutanen za ta samu wata karbuwa fiye da sauran takwarorinta mata a wuin mazan. Sai ga shi kuwa kwalliyar ta biya kudin sabulu, inda kusan kowane namiji da ya zauna ya kalle ta, ko ya tattauna da ita sai da ya yaba ta, ta hanyar ba ta maki mai yawa fiye da mafi yawan matan!

Wannan yana tabbatar mana kenan cewa, kwalliya tana da wata kima ko rawar takawa ta musamman a cikin sha’anin samun karbuwa da girmamawa a wurin wanda ake soyayya ko zama da shi. Kai tsaye dai ka iya cewa matar da duk ta yi sakaci da kwalliya, to ta shiga cikin jerin wadanda suke fuskantar barazanar samun karancin kulawa ko saoyyya daga masoyi ko miji.

Kodayake, abin ba wai ya takaita ga mata kadai ba ne. Domin shi ma kansa Peter ya samu karbuwa fiye da yadda shi kansa ya yi tsammani. Sakamakon samun wannan tagomashin kwalliyar da ya yi. kuma shi kansa ya nuna ya fi jin annashuwa da kuzarin tunkara ko ganawa da matan bayan ya yi wannan kwalliyar.

An Fadi Ba Nauyi.

Kammala wannan jerangiyar ganawa tsakanin mata da mazan, shi ne abin da ya zama raba gardama dangane da batutuwan Farfesa Karl Grammer. Wanda yake da ra’ayin muddun dai fuskokin mutane suka zama iri daya, to za su iya kasancewa masoyan juna, kuma daga cikin mafi dacewar hadi na ma’aurata. Har ma da na Dr. Gleen, da yake ganin mutanen da amsoshinsu suka yi dace da na juna, za su iya kamuwa da son juna.

Domin kusan dukkan wadanda aka yi hasashen za su iya zabar junansu a matsayin masoya a karshen ganawar, sai ga shi sun bayyana kishiyar abin da aka tsammata.

Abin mamaki ma, wasu daga cikin matan, da suke martini game da mazan, yayin ganawa a junansu. Sai ga shi suna cewa ai su sam ba za ma su iya yin soyayya da wanda suka dan yi kamannin da su ba. Saboda ba za su samu wani nishadi a cikin soyayyar ba. kasancewar suna ganin mazan kamar wasu yayyinsu. Sakamakon kamar da suka yi.

Wannan yana nufin abin da Farfesa Karl ya hango, har yake tunanin ya shafi mafi yawan mutane ne, to ya shafi wasu tsirari ne kawai. Don haka bai kai a kafa hujja da shi ba.

Abin Burgewa.

Abu mafi kayatarwa shi ne, bayan kammala wannan gwaje-gwaje, da samuwar wannan sakamako, wanda sam ba a yi tsammanin sa ba. Kai tsaye sai Farfesa Karl ya yarda cewa lallai wannan bincike nasa bai yi nasara ba. Wato abin da ya yi tsammani cewa mace da namijin da suka yi kama da juna a fuska ne za su fi saurin karbar junansu da zama masoya ko ma’aurata, ba hakan yake ba.

Wannan abin a jinjina wa wanda ya yi ne a fagen ilimi. Domin yana banbanta tsakanin halayyar masana da kishiyoyinsu, wadanda ko a musu ba a iya kure su.

“Da farko, bisa la’akari da wasu ma’aurata da suka yi kama da juna. Mun yi tsammanin cewa kasancewar fuskokin mutane (mace da namiji) iri daya, shi ne abin da yake sawa su kamu da son juna. Amma daga karshe sai ga shi hakan bai tabbata ba a cikin bin diddigin. Kishiyar hakan ce ma ta tattaba. Don haka za mu sake sabon lale.” Inji Karl Grammer.

Haduwar Farko Ce Take Tasiri.

Wani muhimmin abu da masanan suka lura da shi, yayin da aka zo wannan gabar shi ne; ganawar farko da ake yi tsakanin mace da namiji ita ce mafi tasiri, domin a cikinta ne komai da zai faru zai faru. Wato dai, mutanen da za su kamu da son juna suna yardar wa kansu hakan ne cikin ‘yan dakiku kadan bayan haduwarsu.

Kawai da zarar mutum ya yi idanu hudu da wadda yake so, cikin abin da bai kai minti daya ba, zai iya ji a ransa, zai so wannan matar ko ba zai so ta ba. Haka nan ita ma matar a lokacin da ta ga mutum, za ta iya ji a ranta cewa za ta so wannan mutumin ko kuwa ba za ta so shi ba.

Wannan yana nuni kenan cewa, dukkan ganawar da wadancan mata da maza suka rika yi a lokut da dama, sam ba su ma da wani amfani. Wannan dai haduwar farko da suka yi, wadda zama kawai suka yi suka kalli juna, ko magana ba su yi ba, ita ta fi tasiri. Fiye da wancan kai ruwa rana da aka dauki lokaci ana yi.

Wannan ma kuma wata alama ce ta cewa binciken da suka dauki tsawon lokaci suna yi, ya ba su ruwa. Kodayake, Farfesa Fanhan yana da abin cewa har yanzu.

Exit mobile version