Me Ya Sa Jarirai Suke Yawan Kuka Da Dare?

Jarirai

Cropped shot of a young mother spending time with her baby girl

Daga Idris Aliyu Daudawa-Kwararra,

Shi dai al’amarin kukan Jarirai da dare wani abu ne wanda yake cima Iyaye musamman ma mata tuwo a kwarya, wannan abin ma ba wai ya tsaya kan mata bane kadai har ma dai wani lokacin da maza. Bama kamar ace idan ita haihuwar ta farko ce manufa anan babu wanda ya san yadda zai yi ya bullo ma al’amarin har ma ya samu wata hanya ta magance hakan.

Manema  labarai sun bada rahoton cewa irin hakan ne take sa wasu Iyayen basu samun damar yin barci da dare, sai dai kawai su kasance idan su biyu suma gaba dayan shi daren , ba domin komai ba, sai don kawai suna neman yadda za su samu shawo kan shi Jaririn har ya samu damar yin barci. Koma dai basu samu damar ta yin barcin ba, a kalla dai sun samu wata natsuwa su da Jaririn lokacin da aka yi sa’a har ya daina yin Kukan.

Al’amarin ya kasance hakan ne domin kuwa da akwai jariran da suke kuka da dare su kuma yi barci da rana, irin hakan shi ne ke sa su Iyaaye su kasance cikin mamakin menene matsalar, yayin da wasu kuma su ke ganin cewa Jaririn watakila  yana jin zafi ne a kan cibiya ko kuma ciwon ciki, da  dai sauransu.

Misis Fatima Umar wata wata ‘yar kasuwa ce kuma uwa ce wadda take da ‘ya’ya yara biyu da take zaune a Abuja, ta bayyana cewar ita a duk lokacin data kusa ta haihu, babban abin da yake damunta shi ne rashin samun damar yin barci da daddare saboda‘ ya’yanta dukan su suna yin kuka ne babu ko fasawa kowanne dare daga haihuwa har  ya  lokacin  da suka kai watanni uku.

Ta ce “wani lokacin na kan yi mamakin cewa jaririna yana ganin wani abu ne wanda yake na daban ne, a gani na shi ne ba wanda ke sa shi kuka sosai.

Ta ci gaba da bayanin cewar “Lokacin da na haifi jariri na ko kuma dana na biyu, har ma na kai shi wurin babban limaminmu don yi masa addu’a, saboda ban fahimci dalilin da zai sa ya ci gaba da kuka ba, da zarar ya kasance karfe 2 na safe har zuwa misalin karfe 4.30 na safe ko kuma karfe 5 na safe.

“Makwabcina ya ci gaba da bani tabbacin cewa zai daina ko kuma kawai na jure na saba da shi kuma da zarar ya kai wata uku, sai kuka ya tsaya kuma za mu iya yin bacci cikin dare

Umar, wacce ta bayyana cewa har yanzu ba ta fahimci dalilin da ya sa wasu jarirai ke kuka da daddare ba, ta kara da cewa “ba tare da wani magani ba, za su daina idan lokacin barin ya yi. Duk da hakan ma shin, menene yake  sa su kuka sosai wanda kuma ba ya bukatar wani magani ne ?, ”ta tambaya.

Misis Amaka Njoku, wata ma’aikaciyar gwamnati ce kuma uwa  ce ga yara biyar da suke zaune a Abuja, ta bayyana cewa duk ‘ya’yanta sun yi kuka da daddare, kuma ta saba da shi kuma kawai tana bukatar sanya abubuwan da take bukata don rashin  samun damar yin bacci.

Njoku ta ce a lokacin da ta haifi  ‘yarta ta farko, akwai ranar da ta kai ta asibitin da ke kusa da gidanta har sau biyu a dare lokacin da taga ba zata iya jure kukan ba amma ma’aikatan jinya sun duba ta sun bayyana mata cewar babu wani abin da yake damunta.

Ta kara da cewa lokacin da ta bayyanawa abokan aikinta mata, da yawa sun ce sun taba shiga irin wannan halin, kuma sun ba ta shawarar kawai ta  ci gaba da yin hakuri ta kuma jira lokacin da  shi Jaririn zai daina yin kukan.

Sai dai kuma, Dokta Eziechila Ressie, wata da take kwararriyar Likita ce ta cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, da ke Jabi, Abuja, ta ce jarirai sabbin haihuwa su kan yi kuka da daddare saboda iskar da suke hadiyewa tare da ruwan nonon da suke sha.

Ta  bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya  ranar Lahadi a Abuja cewa kukan dare da jarirai suke yi tsakanin masu  wata daya da haihuwa zuwa watanni uku shi newani babban al’amarin da taga mata sun faye yin magana dangane da hakn,  inda ta kara da bayanin cewa ” wannan wani abu ne wanda aka saba da jin maganar shi, musamman ma a tsakanin mata sabon aure ko kuma wadanda suka fara haihuwa.”

A cewarta, daya daga cikin dalilan da yasa jarirai ke kuka da daddare shi ne saboda suna iya shan madara mai yawa kuma suna jin zafi a ciyarwar su.

“Kuma ba za su iya jurewa hadiyar ruwan nono tare da iska ba, suna numfasawa suna hadiyewa duk a lokaci guda kuma suna da matsalar hadiye abinci gaba daya tare da iska kamar yadda dai ta bayyana”.

Exit mobile version