Me Ya Sa Kamfanonin Kasa Da Kasa Ke Da Imanin Gudanar Da Harkokinsu A Kasar Sin?
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Kamfanonin Kasa Da Kasa Ke Da Imanin Gudanar Da Harkokinsu A Kasar Sin?

bySulaiman
4 months ago
Sin

An kammala taron shugabannin kamfanoni na kasa da kasa karo na 6 a birnin Qingdao na kasar Sin. A matsayin sa na muhimmin aikin raya tattalin arziki da cinikayya bisa matakin kasa irinsa na farko da kasar Sin ta kafa, musamman ga kamfanonin kasa da kasa, wannan taron ya janyo baki 570 daga kamfanonin kasa da kasa 465, na nahiyoyi 6 na duniya, wanda ya kai wani babban matsayi a tarihi.

Abun lura a nan shi ne, taron mai taken “kamfanonin kasa da kasa da kasar Sin- hada kan duniya da ci nasara tare”, ya nuna yadda kamfanonin kasa da kasa ke daukar kasar Sin a wani muhimmin matsayi yayin da suke tsara shirin gudanar da ayyukansu a duk fadin duniya.

  • Sin Ta Yi Matukar Allah Wadai Da Hare-Haren Da Amurka Ta Kaiwa Iran
  • Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da Rasha Don Daukaka Amincewar Juna Ta Fuskar Siyasa Da Karfafa Muradun Juna

“Bosch yana bukatar kasar Sin, yana bukatar damar yin kirkire-kirkire da saurinsu a nan.” Kalaman shugaban reshen kamfanin Bosch na kasar Jamus dake kasar Sin Xu Daquan ke nan, inda ya bayyana ra’ayin bai daya na kamfanonin kasashen waje, wato yin nazari, da kirkire-kirkire a kasar Sin, matakin dake da muhimmanci a yayin da suke gudanar da harkokinsu a duniya. Ta hanyar yin cikakken amfani da kasuwa, da kwararru, da albarkatun kirkire-kirkire na kasar, za a kai ga ƙarfafa kwarewarsu ta yin takara a duniya.

Yanzu haka, ta hanyar kaddamar da jerin matakan samar da sauki da ba da hidima mai inganci a fannin zuba jari, kasar Sin na kokarin samar da muhalli mafi kyau ga kamfanonin kasashen waje don gudanar da harkokinsu. Yang Lan, babbar daraktar kamfanin Herbalife na kasar Amurka dake kula da harkokin Sin tana ganin cewa, ana ta samun kyautatuwar muhallin kasuwanci a kasar Sin. A cewarta, hakan ya karfafa gwiwarsu ta samun dauwamammen ci gaba a kasar Sin, da ma yin amfani da damammaki yadda ya kamata wajen yin takara.

Bisa irin kwarin gwiwar da suke samu, kamfanonin kasashen waje da ke Sin, suna gaggauta tsara shirin gudanar da harkoki a kasar. Kazalika, bisa yanayin da duniya ke ciki na kara tinkarar ra’ayin kashin kai, da kariyar ciniki, matakan da kamfanonin kasashen waje suke dauka sun nuna cewa, ta hanyar hadewa da kasar Sin ne kadai za su iya dunkulewa da duniya yadda ya kamata, kuma zuba jari a kasar Sin na nufin zuba jari a makomarsu ta nan gaba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Mun Gano Wurare 52 Da Ake Aikata Laifuka A Kano – Janar Mai Adda’u

Mun Gano Wurare 52 Da Ake Aikata Laifuka A Kano - Janar Mai Adda’u

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version