Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Me Ya Sa Kasar Sin Ta Iya Samun Nasara Mai Armashi Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi?

Published

on

Yau ranar 26 ga watan Yuli shekarar 2020, rana ce ta yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa. Shin a wannan fanni, wane irin ci gaban da Sin ta samu? Kafin amsa wannan tambaya, ina son in gaya muku wani labari.

Birnin Lincang dake kudu maso yammacin lardin Yunan, yana dab da kasar Myamar, tsawon layin iyaka dake tsakanin kasashen biyu a wannan wuri ya kai kilomita 290.79, saboda wurin yana kusa da sansanin sayar da miyagun kwayoyi na “Golden Triangle”, wato wurin dake kan iyakar kasashen Myamar da Thailand da kuma Laos. Sin ta kafa wani rukunin yaki da miyagun kwayoyi a wannan yanki, tun daga shekarar 1982.
Gudanar da aikin yaki da miyagun kwayoyi a kan iyakar kasashe akwai matukar wuya, saboda masu fataucin miyagun kwayoyi su kan boye cikin gandun daji, tare da daukar makamai masu karfi, duk da ganin irin wadannan mawuyancin hali, rukunin birnin Lincang ya cafke masu fatauci, ko masu saye, ko masu harhada miyagun kwayoyi fiye da 8500, ya kuma kwace miyagun kwayoyi fiye da ton 2400 tun daga shekarar 2015.
Ban da wannan kuma, yawan mutanen da aka cafke a wannan fanni da suke da alaka da birnin Lincang ya ragu da kashi 50%. Birnin Lincang, wani kashi ne daga cikin tsarin yaki da miyagun kwayoyin da Sin ta tsara, duk fadin kasar na hadin kansu don yin iyakacin kokarin yaki da miyagun kwayoyi da tabbatar tsaron jama’a.
Sin tana da ’yan sanda da kuma sojoji masu kishin kasa, suna fahimtar nauyin dake wuyansu matuka, wato kare tsaron kasa da ba da tabbaci ga lafiyar jama’a. Gwamnatin kasar Sin kuma tana mai da hankali matuka kan wannan aiki.
A ran 23 ga watan Yuni na shekarar 2020, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da kungiyoyi ko daidaikun mutane, wadanda suke ba da muhimmiyar gudunmawa wajen yaki da miyagun kwayoyi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar tare da ba da jawabi, inda ya ba da alkiblar yaki da miyagun kwayoyin da za a bi nan gaba. Hakan ya sa, hukumomi daban-daban masu yaki da miyagun kwayoyi, sun tabbatar da ruhi da kuma manufofin shugaba Xi ta fuskar yaki da miyagun kwayoyi, an kuma koyi abubuwa daga wadannan kungiyoyi da daidakun mutane, don kafa wani tsarin yaki da miyagun kwayoyi a duk fadin kasar baki daya, ta yin amfani da dabarun kimiya da fasaha na zamani, ta yadda za a ba da tabbaci ga lafiyar jiki da tsaron jama’a.
Ban da wannan kuma, shekarun baya-baya nan, Sin ta kara hadin kai da daukar matakai masu inganci da sauran kasashe a wannan fanni, da ilmantar da jama’a don hana su mu’amala da miyagun kwayoyi, har ma da daukar matakan tallafawa matalauta, don hana su yin cinikin miyagun kwayoyi saboda rashin kudin shiga.
Game da mutane da suke shan miyagun kwayoyi kuwa, Sin ta kafa kungiyoyi masu kula da su, don hana su shan miyagun kwayoyi, da taimakawa musu sake dawowa cikin al’umma. An ba da kididdigar cewa, ya zuwa karshen shekarar 2019, yawan mutanen da suka daina amfani da miyagun kwayoyi, har suka kai shekaru 3 da kaurace wa kwayoyin, ya kai mutum miliyan 2.53, wanda ya ninka sau 2.2 bisa na shekarar 2015. Har ila yau, yawan masu amfani da miyagun kwayoyi ya ragu da kashi 8.43% bisa na shekarar 2015, adadin ya ragu matuka cikin shekaru 2 a jere.
Saboda ganin irin wadannan ci gaba da aka samu, shugaban na Sin Xi Jinping, ya jinjinawa hukumomi da daidaikun al’ummar kasar, da ke tsayawa tsayin daka wajen yaki da fatauci, da ta’ammali da miyagun kwayoyi a ran 23 ga wannan wata da muke ciki, tare kuma da yin kira ga sassan masu ruwa da tsaki a fannin yaki da fatauci, da amfani da miyagun kwayoyi, da su kara azama wajen cimma nasarorin da aka sanya gaba. Kuma a yau 26 ga wata, shugaba Xi ya jadadda wajibcin cimma nasarar yaki da miyagun kwayoyi. Yana mai cewa, ba za a dakatar da wannan aiki ba idan ba a samu nasara ba, saboda wannan aiki na da alaka matuka ga zaman rayuwar jama’a.
To, a yanzu ko mun fahimci dalilin da ya sa Sin ta iya samun nasara mai armashi wajen yaki da miyagun kwayoyi? (Mai rubuta: Amina Xu)

Advertisement

labarai