Abba Ibrahim Wada">

Me Ya Sa Suares Zai Bar Barcelona?

Bayan kakar wasa shida da dan wasa Luis Suarez ya yi a Barcelona ya kuma lashe gasar La Liga guda hudu da gasar cin kofin zakarun turai na Champions League da kwallo 198 daya zura a kungiyar, yanzu dan wasan zai koma Atletico Madrid a bana.
Suarez ya buga wa Barcelona wasanni 36 a kakar wasan data gabata ta 2019 zuwa 2020 sannan ya kuma ci mata kwallo 21, sai dai ya yi fama da jinya ta wajen watanni hudu wanda hakan yasa bai samu damar zura kwallaye da yawa ba.
A cikin watan Janairun shekarar 2020 sai da Suarez ya yi jinyar wata hudu, dalilin da ya sa dan wasan bai buga wa tawagar Uruguay karawar neman shiga kofin duniya a watan Maris bad a kasashen Brazil da Peru.
Barcelona ta karkare kakar wasan shekarar 2019 zuwa 2020 ba tare da lashe kofi ba, bayan da ta yi ta biyu a La Ligar da aka karkare wacce Real Madrid ta lashe kuma hakan ne ya sa kungiyar ta tsara shirye-shiryen da zai sa ta taka rawar gani a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021.
Barcelona ta sayi wasu daga cikin ‘yan wasan da take ganin zasu taimaka mata a kakar wasa m,ai zuwa inda ta dauki Pedri Las daga Palmas sai Trincao daga kungiyar Braga ta kasar Portugal sai  Matheus Fernandes daga balladolid da kuma Miralem Pjanic daga Jubentus kan fam miliyan 54.
Har ila yau kungiyar ta sayar da wasu daga cikin ‘yan wasanta wadanda take ganin ba zata iya amfani dasu ba a wannan kakar da aka fara inda dan wasa Marc Cucurella ta koma Getafe sai  Guillem Jaime wanda ya tafi Castellon sai Iban Rakitic wanda ya koma tsohuwar kungiyarsa ta  Sebilla ya yinda Arthur Meslo ya koma zuwa Jubentus sai Dani Morer shi kuma zuwa Famalicao sannan Arturo bidal zuwa Inter Milan da Jorge Cuenca zuwa billarreal sai kuma dan kasar Portugal Nelson Semedo wanda ya kammala komawa Wolberhampton ta kasar Ingila.
Haka kuma Barcelona ta dauki sabon mai koyarwa Ronald Koeman a bana, wanda ya fayyace ba zai yi aiki da dan kwallon tawagar Uruguay din ba, duk da cewar Suarez na son ci gaba da zama a kungiyar koda zaman benci ne.
An yi ta rade-radin cewar kungiyoyi da dama na zawarcin tsohon dan kwallon Liberpool din, kuma a wannan makon batun zuwansa Jubentus ya bi ruwa saboda batun fasfo wanda aka bayyana cewa yayi satar amsa wajen neman shaidar zama a kasar ta Italiya.
Suarez ya amince a rage masa albashi a kungiyar Atletico Madrid duk don ya bar Barcelona a bana, an kuma fahimci cewar shugaban Barcelona, Josep Maria bai so a sayar da dan kwallon ba saboda yana son zamansa a kungiyar sakamakon halin rashin kudin da kungiyar ta shiga.
Shugaban ya yi taro da wakilan Suarez kan cewar yana bukatar dan wasan ya ci gaba da zama a Barcelona, shi kuwa dan kwallon ya ce zai sanar da ‘yan jarida halin da ake ciki kan batun barin kungiyar.
Kawo yanzu Atletico Madrid abokiyar hamayyar Barcelona za ta biya Suarez mai shekara 33 Yuro miliyan hudu, hakan ma idan kungiyar ta taka rawar gani a gasar cin kofin zakarun turai na bana da za’a fara wato Champions League.
Amma duk da haka Suarez zai karbi rabin Yuro miliyan 30 a shekara a Atletico, abinda ake ba shi a Barcelona matakin da ake ganin ba karamin nakasu dan wasan ya samu ba akan maganar albashi.
dan kwallon na Uruguay ya koma Barcelona daga Liberpool shekara shida da suka wuce kan fam miliyan 74 daga Liberpool ya kuma taka rawar gani a kungiyar ta Camp Nou da ya yi wasanni 283 a lokacin da suka addabi duk kungiyar da suka hadu da ita a lokacin tare da Messi da Neymar.
dan wasan ya lashe gasar Copa del Rey guda hudu da kofin zakarun nahiyoyin duniya da ake kira Club World Cup a shekarar 2015 kuma har yanzu yana wakiltar tawagar ‘yan wasan kasar Uruguay a wasannin kasashe.
Wasannin da Barcelona za ta fara buga wa a La Liga ta 2020-21:
Lahadi 27 ga Satumba 2020
Barcelona da billarreal
Laraba 30 ga Satumba 2020
Celta bigo da Barcelona
Lahadi 04 ga Oktoba 2020
Barcelona da Sebilla
Lahadi 18ga Oktoba 2020
Getafe da Barcelona

Exit mobile version