CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Me Ya Sa ‘Yan Siyasan Kasashen Yammacin Duniya Suke Mara Wa Scott Morrison Baya?

by CRI Hausa
December 3, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Me Ya Sa ‘Yan Siyasan Kasashen Yammacin Duniya Suke Mara Wa Scott Morrison Baya?
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kwanan baya, an yi Allah wadai da babbar murya kan yadda sojojin kasar Autraliya suka kashe wadanda ba su ji ba su gani ba a kasar Afghanistan. Firaministan Australiya Scott Morrison ya ce dole ne kasar Sin ta nemi gafara daga kasarsa saboda wani zanen da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya wallafa a shafinsa na Twitter dangane da yadda sojojin Australiya suka kashe fararen hula a Afghanistan.

Abin da mista Morrison ya yi tamkar abin dariya ne. Amma wasu ’yan siyasa na kawayen Australiya da kafofin yada labaru na yammacin duniya sun tayar da jijiyar wuya, inda suka yi shelar cewa, za su hada hannu da Australiya wajen yaki da kasar Sin. To, ina dalilinsu?
Da farko suna kokarin taimaka wa Australiya ne, don ta dauke hankalin jama’a daga abin da sojojin kasar suka aikata a Afghanistan da kuma boye laifuffukan da suka aikata. Haka kuma, a matsayinsu na kawayen Australiya, Amurka da Birtaniya suna son hada kai da Australiya su nuna wa kasar Sin karfinsu, a yunkurin boye laifuffukan da suka aikata a Afghanistan da kuma bata sunansu na masu rajin kare hakkin dan Adam. Wani dalili mai muhimmanci shi ne, wasu ’yan siyasan kasashen yammacin duniya masu taurin kai wadanda suke kallon kasar Sin bisa tunaninsu, suna ganin cewa, suna da da’a, suna da ikon yanke hukunci kan wasu. Su kan soki kasar Sin da sauran kasashen duniya, amma ba su son kasar Sin da sauran kasashe su soki laifuffukan da suka aikata ba.
Wadannan ’yan siyasan kasashen yammacin duniya wadanda suke farin ciki da ganin an tada hankali a duniya, suna kara mara wa mista Morrison baya, to, abin da suke yi, suna kara sanya kasashen duniya su kara sanin laifuffukan da sojojin Australiya suka aikata a Afghanistan, sa’an nan suna gane laifuffukan da kasashensu suka aikata da kuma yadda suke nuna girman kai da yin fuska biyu a wasu fannoni. (Tasallah Yuan)

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Sin Ta Gabatar Da Takardar Bayani Kan Ba Da Tabbaci Ga Samar Da Aikin Yi A Jihar Xinjiang

Next Post

An Taso Keyar Abdulrasheed Maina Daga Nijar

RelatedPosts

Shugaba Xi Ya Duba Shirye-shiryen Da Ake Yi Na Karbar Bakuncin Gasar Olympic Ta Birnin Beijing A 2022

Shugaba Xi Ya Duba Shirye-shiryen Da Ake Yi Na Karbar Bakuncin Gasar Olympic Ta Birnin Beijing A 2022

by CRI Hausa
9 hours ago
0

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya duba shirye shiryen da...

Adadin Wayoyin Hannu Masu Fasahar 5G Da Sin Ta Fitar Ya Kai Miliyan 163 A Shekarar 2020

Adadin Wayoyin Hannu Masu Fasahar 5G Da Sin Ta Fitar Ya Kai Miliyan 163 A Shekarar 2020

by CRI Hausa
10 hours ago
0

Sabbin alkaluman cibiyar nazarin fasahar sadarwa ta kasar Sin CAICT...

GDPn Kasar Sin Ya Karu Da Kaso 2.3 A Shekarar 2020

GDPn Kasar Sin Ya Karu Da Kaso 2.3 A Shekarar 2020

by CRI Hausa
10 hours ago
0

Wasu alkaluma da hukumar kididdigar kasar Sin (NBS) ta fitar...

Next Post
Abdulrasheed

An Taso Keyar Abdulrasheed Maina Daga Nijar

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version