Abba Ibrahim Wada" />

Me Ya Sa ’Yan Wasan Real Madrid Suke Yawan Zuwa Jinya?

real madrid

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fafata wasa da kungiyar kwallon kafa ta Getafe a kwantan wasan mako na farko a gasar Laliga da suka fafata ranar Talata kuma Real Madrid ta samu nasara da ci 2-0 ta hannun dan wasa Karim Benzema da kuma Edourdo Mendy.

Sai dai kuma Real Madrid na fuskantar kalubale, bayan da ‘yan wasanta da dama ke jinya a kakar wasa ta bana wanda hakan yana daya daga cikin dalilan da suka sanya kungiyar bata abin kirki a musamman kana nan wasanni.

Dan wasa Eder Militao da kuma Albaro Odriozola su ne na baya-bayan nan da suka shiga jerin masu jinya a kungiyar wanda hakan yasa kociyan kungiyar, Zinadine Zidane ya shiga tasku na zabar ‘yan wasan da zai dinga buga wasa dasu.

‘Yan wasan da ke jinya kawo yanzu sun hada da dan wasan baya kuma kaftin din kungiyar Sergio Ramos da Dani Carbajal da Lucas Bazkuez da Eder Militao da Fede Balberde da Eden Hazard da kuma Rodrygo.

Haka kuma wani dan wasan Albaro Odriozola ya yi rauni, ya yin da Toni Kroos ke hutun hukunci kan kati biyar aka ba shi, saboda haka bai buga wasan Getafe bad a suka fafata a daren Talata.

Real Madrid ta damu da raunin da ‘yan wasanta ke yi da ya kai sau 38, ko da yake ana alakanta wasannin da ake yi kusa da kusa, sakamakon cutar korona da ta haddasa saboda ba’a fara kakar wasa ta bana bad a wuri.

Haka kuma Real Madrid ba ta sayi dan kwallo ba a kakar bana, saboda haka ‘yan wasa ba sa samun hutu yadda ya kamata, har ta kai hutu shi ne idan ka yi rauni kuma a kalla dai ‘yan kwallon Real Madrid 20 ne suka yi rauni ko dai a karon farko wasu ma sau bibiyu a kakar wasa ta 2020 zuwa ta 2021.

Sai dai abin da ya kamata kungiyar ta bincika shi ne ko ‘yan kwallon na yin rauni ne sakamakon yadda ake jinyar mutum ya koma cikin fili da wuri ba tare day agama warkewa ba a hankali sakamakon bukatar ‘yan wasan da kungiyar takeyi?

Ko kuma rashin samun motsa jiki da ya dace da zai yi daidai da wasan da dan kwallo zai fuskanta kafin buga wasa saboda wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar sunji rauni sau biyu ko sama da haka a wannan kakar.

Wani lokacin ‘yan kwallo na sawa kansu matsi ganin sun sa kwazon da zai kai kungiyar wani mataki da hakan ya sa mutum ya yi rauni wanda kuma hakan babbar illa ce ga kungiyar da kuma lafiyar ‘yan wasa kamar yadda likitoci suke bayyana wa.

Real Madrid ita ce da kofin La Liga na bara, sai dai tana ta biyu a teburi, bayan da Atletico ke jan ragama sai kuma Barcelona ta uku sannan idan har Real Madrid ba ta kara sa kaimi ba a bana za ta iya karkare kakar ba tare da lashe kofi ba, domin ta rasa Spanish Super Cup da Copa del Rel kawo yanzu.

Yanzu dai kofin da Real Madrid ke hari shi ne na Champions League da ta kai zagaye na biyu da za ta fafata da Atalanta cikin watan nan na Fabrairu haka kuma ana fafatawa da ita a La Liga, koda yake Atletico Madrid ta bata tazarar maki bakwai, bayan da aka buga wasannin mako na 22 yanzu.

 

Exit mobile version