Shugabannin Turai da na Gabas ta tsakiya sun yi maraba da yarjejeniyar da Amurka ta tsara na tabbatar da zaman lafiya a Gaza.
Shugaba Trump ya ja kunnen Hamas kan kada ta sake ta ki amincewa da yarjejeniyar.
- Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
- NAFDAC Ta Rufe Manyan Shaguna 2 Na Ƴan China A Abuja
Shawarwarin da shugaban Amurka Donald Trump da Firaiminstan Isra’ila Benjamin Netanyahu suka amince da su sun bukaci kawo karshen yakin nan take da sakin ‘yan Isra’ila 20 da har yanzu ke raye cikin wadanda aka yi garkuwa da su.
Sannan a mayar da gawarwakin sauran duka a cikin kwana uku, yayin da Isra’ila za ta saki daruruwan Falasdinawa da take rike da su a gidajen yarinta.
Yarjejeniyar ta kuma ce Hamas ba za ta taka wata rawa wajen tafiyar da mulkin Gaza ba, sai dai ta bar kofa a bude na yiwuwar kafa kasar Falasdinu, kodayake Netanyahu ya yi fatali da wannan.
Cikin wata hira da kafar yada labarai ta Adiou ranar Lahadi, Shugaba Trump ya ce ”Mutane da dama ne ke taruwa domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya, don haka ya kamata mu tabbatar da ita,”.
Ya kara da cewa yana sane da irin kokarin aiki tare da kasashen Larabawa ke yi wajen kawo karshen yakin, sannan Hamas ta nuna alamun yin sulhu ta hanyar masu shiga tsakani.
”Kasashen Larabawa na son zaman lafiya, Isra’ila ma na so, Bibi (Netanyahu) na son zaman lafiya.”
Shugaba Trump ya ce daftarin zaman lafiyar da ya gabatar, ba kawo karshen yakin kawai zai yi ba, har ma da samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
“Idan muka cimma wannan nasara, zai zama babban abin tunawa ga Isra’ila da ma yankin Gabas ta Tsakiya, don haka dole a cimma hakan”.
Muhimman kudurorin yarjejeniyar
Kafar yada labaran Adios ta ce shirin na Trump ya kunshi kudurori 21 da suka kunshi:
Sakin duka ISra’ilawan da Hamas ke garkuwa da su cikin sa’o’i 48 na dakatar da wutar.
Dawwamammen dakatar da wuta da kuma janyewar dakarun Isra’ila daga zirin Gaza sannu a hankali.
Sakin fursunonin Falasdinawa kusan 250 da ke zaman daurin rai da rai a gidajen yarin Isra’ila, da kuma wasu kusan 2,000 da aka tsare bayan harin 7 ga watan Oktoba.
Kafa wani kwamitin gudanar da mulkin Gaza, wanda ba zai kunshi mambobin Hamas a ciki ba.
Kwamitin zai kunshi wasu shugabannin kasashen duniya da majalisar kungiyar kasashen Larabawa da wakilan hukumar Falasdinawa tare da wasu kwararru a yankin.
Samar da jami’an tsaron hadin gwiwa da za su kunshi Falasdinawa da sojoji daga wasu kasashen Larabawa da Musulmai.
Saka jari daga kasashen Larabawa domin sake gina Gaza. Kwace makaman Hamas tare da lalata rumbunan ajiyar manyan makamansu. Yin afuwa da mambobin kungiyar da suka tuba.
Dakatar da Isra’ila daga mamaye Gabar Yamma ko wani sashe na Gaza.
Alkawarin bude kofar yiwuwar kafa kasar Falasdinu bayan yin garambawul ga hukumar Falasdinawa.
Alkawarin kada Isra’ila ta sake kai wa Katar hari a nan gaba.
Tuni dai aka mika wa Hamas daftarin yarjejeniya, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Katar ta tabbara. Cikin wata sanarwa da kakain ma’aikatar ya fitar, Majed al-Ansari ya ce ”Wakilan kungiyar sun alkawarta yin nazari na tsanaki kan daftarin kafin sanar da matakin da za ta dauka a kai.
Majed al-Ansari ya ce Katar ta shiya wata tattaunawa da masu shiga tsakani na kungiyar Hamas da jami’an Turkiyya a yau domin tattauna batun.
A baya dai kungiyar ta sha nanata cewa za ta martaba duk wata yarjejeniya da za ta kunshi kare al’ummar Falasdinu.
‘Abin da muke so shi ne dakatar da yakin’
Kwana guda bayan sanar da daftarin kawo karshen yakin, al’ummar Gaza na ci gaba da bayyana fatansu game da yarjejeniyar.
Esraa mai shekara 23 ta ce ko bacci ba ta iya yi ba saboda samun labarin daftarin dakatar da yakin.
“A dauka an kulla yarjejeniyar dakatar da yakin ne, ashe gadftarin ne kawai”, kamar yadda ta bayyana ta wayar.
Esraa ta ce ta yi imanin cewa an tsara daftarin ne bisa “muradun Isra’ila” amma duk da haka al’ummar Gaza na son zaman lafiya, don haka za su amince da duk abin da zai sa yakin ya zo karshe.
Can ma a kudancin Gaza, wata mahaifiyar yara hudu ta fada mana cewa ba ta da wani zabi illa ta goyi bayan daftarin.
“Duk da rashin adalcin da aka yi wa mutanenmu, mu kawai abin da muke so shi ne kawo karshen yakin”, kamar yadda ta bayyana mana sa WhatsApp.
“Muna matukar shan wahala, kuma ba mu da damar ci gaba da rayuwa face amince da wannan daftarin, ko a wane yanayi, saboda muna cikin wahala.”
Matsayin hukumar Falasdinawa kan daftarin
Hukumar kula da yankunan Falasdinawa ta yi maraba da daftarin na Amurka.
Cikin wata sanarwa da ta kamfanin dillancin labarai na Wafa ya wallafa ya ce hukumar a shirye take wajen yin aiki da Amurka da sauran kasashen yankin Gabas ta Tsakiya domin kawo karshen yakin Gaza.
Hukumar Falasdinawan ta ce a shirye take wajen tabbatar da zaman lafiyar yankin domin samun damar shigar da agaji zuwa Gaza tare da sakin isra’ialwan da ake garkuwa da su.
Sanarwar ta kuma ce hukumar na da muradin gudanar da sabbin zabuka a cikin shekara guda bayan kare yakin tare da kafa tsaron yankin.
“Mun tabbatar da kudurinmu na son dimokradiyya da kafuwar kasarmu maras barazanar makamai da kuma mika mulki ga sabuwar zababbiyar gwamnati”, in ji sanarwa.
Hukumar Falasdinawa, karkashin jagorancin shugabanta, Mahmoud Abbas – da ke samun amincewa kasashen duniya ce – ke mulkin Gabar yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.
Zaman lafiyar Gaza na hannun Hamas – Isra’ila
Ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Sa’ar, ya ce kasarsa na fatan kawo karshen yakin sai dai idan Hamas ce ba ta so hakan ba.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a Belgrade, mista Sa’ar ya yi ikirarin cewa Hamas ce take kawo jan kafa a kokarin kawo karshen yakin Gaza tun kafin yanzu.
”A yanzu ya rage nata ko za ta amince da daftarin ko kuma a a?”, in ji shi.
Ya ce Isra’ila na son a sako mata duka ‘yankasarta da Hamas ke garkuwa da su tare da karbe duka makaman Hamas ta yadda ba za ta sake zama barazana ga Isra’ila a nan gaba ba. Daga BBC Hausa