Me Yasa Shugaba Buhari Ya Ke Tarawa Kansa Makiya?

Daga Kwamared Sunusi Mailafiya

Ina iya tuna shekarar 2011 a Jihar Kano, ranar da Shugaba Buharin yazo yakin neman zabe lokacin yana jam’iyyar CPC. Ina daidai anguwar Fagge yayin da Attajiri Muhammadu Abacha ya wuce da gwanon motoncinsa. Akwai Lawal Jafaru Isa da shi M ABacha din duka karkashin jam’iyyar ta APC, to amma abin mamaki shine yadda Buharin yaki daga hannun kowanne daga cikinsu saboda rikicin zaben cikin gida na futar da dan takara, duk da cewa Koda ya daga hannun kowa, ba lalle ne a iya kayar da Kwankwaso ba lokacin daya dawo neman takara. Tun a wannan lokacin ya Kamata Shugaba Buhari ya fara tarawa kansa makiya, saboda wannan al’amari, amma dai babu abinda ya faru. Thank God, har Jihar Nassarawa Tanko Almakura ya kawowa jam’iyyar ta CPC.
Duka dai a shekarar ta 2011 bayan an fadi sakamakon zabe, matasa daga jihohi da dama sun gabatar da zanga-zanga saboda kawai suna ganin cewa Buhari ne ya cinye wannan zaben. Ganin idona yan Sanda suka dinga harbi a kan titin gidan Marigayi Isiyaka Rabiu. A wannan lokacin anyi asarar matasa da dama, amma saboda dai a zauna lafiya, Buharin ya Jajanta mutuwar, tare da korar da wannan danyen aikin da matasa sukayi daga gareshi, tun anan ma ya Kamata ya tara makiya, amma bai yi ba. Thank God, Yayi hakan ne saboda al’amarine daya shafi tsaron kasa.
Idan muka ajje duka Wadancan tarihan, mu kalli al’amarin da ake ciki yanzu. Duk wani cin buri da mukayi akan Shugabancin Buhari, shekaru kusan shida (6) kusan har yanzu babu wanda ya cika. Da mu din, da Babanmu Mai Gaskiya a wannan lokacin mun soki Gwamnatin PDP da cin hanci, mun soketa da karin kudin fan fetur (janye tallafin fetur), mun sokesu akan rashin tsaro na kabilanci da na Boko haram, mun sokesu akan rashin wuta, ruwa da ingantaccen ilimi, mun sokesu akan yajin aikin Malaman Jami’o’i da na Lafiya, mun sokesu akan kaza da kaza da kaza…….Dukansu a yanzu babu abinda idanuwanmu basu gane mana ba. Yajin aikin ASUU ko ASUP din, farashin man fetur ne, rashin tsaron ne ko almundahana da kudin Gwamnati, wanne ne yanzu idanuwanmu basu gane mana ba. Duk wani alwashin mu, cika bakinmu, has ashen mu da muradun mu idan Shugaba Buhari mai gaskiya ya hau kan mulki sun kau a yanzu tun daga kan Ma’aikatan Gwamnati, Dalibai, Yan Kasuwa, Manoma, Masu Kudi, Tsakatsaki, Talakawa har ma da yan zaman banza dukansu yau sunyi laushi, sun fara hakura da duk wani canji karkashin wannan Gwamnatin da suka bawa yardar su abaya.
A hankali-A hankali Shugaba Buhari ya kasa gane cewa yana tarawa kansa makiya. Yan Jam’iyyar adawa sun kara tsananin adawa saboda an kasa nuna musu cewa mulkin jam’iyyar su na baya zalunci ne. Mabiyan jam’iyyar APC kuwa, wanda akayi duk wata gwagwarmayar kafa mulki dasu, suma yanzu sun juyawa Gwamnati da Shugaba Buhari baya, saboda dukan ya wuce kan sauran al’umma, har kawunan su. Duk wasu masoya na kusa, ko na nesa da Buharin yake dasu, yanzu sunyi kaura daga gareshi. Ina Naja’atu Mohd, kucemin daya, ina Faruk Adamu Jigawa, kucemin biyu, ina Haruna Zago, ina Buba Galadima, ina……… duka yanzu sun juya masa baya. Duk Wata Kungiya da abaya da ta marawa Buharin, yau sunyi hannun riga dashi saboda yanayin mulkin da ake gabatarwa, Buhari ya bata da ASUU, ya bata da ASUP, ya bata da NLC, ya bata da ACF, ga Kungiyoyin nan barkatai da suka dinga goyon bayan Buhari saboda suna ganin sauki zaizo, amma yau duka sun zama makiyan Buhari. Kaso 70 na al’ummar da suka dinga turawa Baba Buhari kudi ta katin waya a matsayin tallafin su, yau sun juya masa baya, kai bar ta Wadancan duka ma, daidai da Uwargidan Shugaba Buharin sai data juya masa baya tare da fitowa duniya tana sukar salon mulkin Shugaba Buharin. Babu matasa, babu tsofaffi babu dalibai, kowa yanzu ya zama kamar dan jam’iyyar adawa.
Kusan kullum yanzu kasar nan cikin asarar rayuka ake yi sakamakon kashe-kashen Yan Ta’adda. Ko a satin daya gabata sai da Gwamnan Jihar Naija ya ayyana cewar wani bigire daga Jihar tasa Yan Ta’adda sun kafa tutar su. Ga dalibai daga Jihar Kaduna da masu garkuwa suka sace, suna ta yi musu kidan dauki dai-dai, abin abun tausayi da tashin hankali, ga wasu a Zaria, ga wasu sama da Hamsin da aka binne lokaci daya satin daya gabata a Jihar Zamfara, ga Geidam ta Jihar Yobe da Yan ta’addan Boko haram suka uzzurawa a cikin satin nan.
Yanzu babu wanda zai iya lissafa adadin al’ummar da aka salwantar tun daga hawan mulkin Shugaba Buharin. Boko haram tana nan, ga kuma karin masu garkuwa da mutane, ga kashe-kashen yan Arewa mazauna Kudancin kasar nan. Babban abin damuwar shine yadda Gwamnati tun wannan ruwan kisan mummuken da akeyi, ta kasa sanya dokar ta baci (state of emergency) akan tsaron, wanda hakan shine zai bada damar a fuskanci Yan ta’addan da karfi.
Gwamnatin Buhari tayi kokari wajen canza madafun iko na bangaren tsaro. Shugabannin Rundunar Tsaron kasar nan na baya sun gaza wajen yaki da Ta’addanci. Yanzu da Gwamnati ta canza su, Kamata yayi abasu duk Wata gudummawa da tafi ta baya, to amma sai gashi da labari mafi muni zasu fara, inda mai bawa Shugaban kasa shawara akan tsaro Baba Gana Munguno yace kudaden da aka ware don siyo makamai da sauran kayan yaki, to fa wannan kudin sunyi batan dabo, kamar dai yadda ya faru zamanin Goodluck Ebele da wasu yan jam’iyyar PDP suka kididdiba kudaden makamai don siyowa kansu kujerar mulki.
Ya dai Kamata Gwamnatin APC ta gane cewar yanzu tarin makiyan da ta tara, sunfi masoyan da take dasu. Duk wasu masoya da suka tsayawa wannan jam’iyyar da Shugaba Buhari, a yanzu suma sun gano kasawar wannan Gwamnatin ta bangarori da dama. Tun daga matakin tattalin arzikin kasa, cin hanci da rashawa, da kuma uwa-uba tsaron. Idan har Gwamnatin Shugaba Buhari tana so ta dawo da martabar ta da kimar ta, dole ne sai ta saisaita al’amuran kasar nan, musamman ta bangaren tsaro. Walau dai ta kawo sababbun dabaru, ko kuma ta sanya dokar ta baci. Sannan al’umma zasu gane cewar lalle Gwamnatin kasar da gaske take, amma a irin wannan yanayin da ake ciki, Shugaban kasar yaja bakinsa yayi shiru, Yan Majalisun kasar suma banda yanzu da al’ummar su suka uzzura musu, amma sam basu shirya daukan wani matakin gaggawa akan sha’anin na tsaro ba.
A yanzu da Hukumar zabe ta kasa INEC ta futar da ranar zabe na shekarar 2023, to yar manuniya ce dake nuna cewa Gwamnatin kasar nan an fara kirga mata Kwanakin da zata kare. Kuma burin jam’iyya mai mulki shine ta kuma gaje kujerar Shugaban kasa. To ya Kamata ta sani, idan har akaci gaba da tafiya ahaka, to akwai tsoro da tashin hankali ma ace zaben kasar ya faru a irin wannan yanayin na lalacewar tsaro a kasar gabaki daya. Dole ne Gwamnatin Shugaba Buhari ta dawo da martabar ba, ta hanyar kawo karshen matsalar tsaro daya kuma gurguncewa a karkashin mulkin nata.

Exit mobile version