Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Me Ziyarar Xi Jinping A Lardin Shaanxi Ta Gaya Mana?

Published

on

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a lardin Shaanxi dake yammacin kasar Sin, daga ranar 20 zuwa ranar 23 ga wata, wurin da ya kasance zango na biyar da shugaba Xi ya kai ziyara, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin.

Yayin ziyarar tasa a lardin, shugaba Xi Jinping ya ziyarci kamfanin motoci na lardin Shaanxi, wanda ya kasance kamfanin kire-kire mafi girma a arewa maso yammacin kasar Sin, kuma kamfani kadai dake samar da motoci masu amfani da wutar lantarki na kasuwanci. Kana, kamfanonin dake da nasaba da wannan kamfani suna da yawa, shi ya sa, farfadowar ayyuka a kamfanin motocin Shaanxi za ta samar da damammaki ga kamfanoni masu nasaba da shi, da ma wasu kanana da matsakaitan kamfanoni wajen dawowa bakin aiki.

Haka kuma, shugaba Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a wasu yankunan masana’antu, unguwanni, asibitoci da makarantu, wadanda suke ba da muhimmanci ta fuskar harkokin masana’antu, samar da guraben aikin yi, da ba da ilmi, da aikin jinya, da kuma taimakawa matalauta da dai sauransu.

Bugu da kari, a rana ta biyu ta ziyarar shugaba Xi a lardin Shaanxi, lardin Qinghai na kasar Sin ya sanar da cewa, dukkanin gundumominsa sun kawar da talauci a hukumance. Ya zuwa yanzu, akwai larduna, yankuna da birane gaba daya guda 12 da su kawar da talaucinsu baki daya, kuma gundumomi masu fama da talauci kaso 80% sun kawar da talaucinsu.

Don gane haka, za a fahimci wani muhimmin labarin da ziyarar Xi Jinping a lardin Shaanxi ta samar mana, wato, “an yi imani da cewa, za mu cimma burinmu na bana a fannin kawar da talauci bisa dukkanin fannoni.”

Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya ce, za mu samu gagarumin ci gaba bayan aukuwar hadari mai tsanani, al’ummomin kasar Sin su kan samu ci gabansu cikin mawuyacin hali. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: