Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Mece Ce Matsalar Chelsea?

by Abba Ibrahim Wada
January 6, 2021
in WASANNI
2 min read
Aure-aure
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ranar Lahadi kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sha kashi a hannun Manchester City da ci 3-1 a Stamford Bridge a wasan mako na 17 a gasar Premier League rashin nasarar da kungiyar ta yi ya sa ta koma ta takwas a teburi da maki 26, bayan buga wasa 17 a kakar bana.

Kuma wasanni na biyar kenan da aka doke Chelsea a Premier, bayan cin wasa bakwai da canjaras biyar da cin kwallo 32 aka zura mata 21 a ragarta a gasar ta bana duk da cewa da farko anyi zaton Chelsea zata iya lashe gasar firimiyar bana.

samndaads

Tun da aka fara kakar bana masu sharhin wasanni suka sa Chelsea tana daga cikin kungiyar da za ta kalubalanci kungiyar Liverpool da Tottenham wajen lashe kofin Premier League na kakar wasa ta bana wato  2020 zuwa 2021.

Sai dai kuma alkaluma sun sauya tun bayan da Eberton ta yi nasara a kan Chelsea ranar 12 ga watan Disamba, wadda ta kawo karshen wasanni 17 da kungiyar ta Stamford Bridge ta yi a dukkan karawa ba tare da an doke ta ba.

Cikin maki 18 da ya kamata Chelsea ta hada da kyar da gumin goshi ta samu hudu, kuma a lokacin Sheffield United ta yi rashin nasara wasa shida sai West Brom da biyar sai Chelsea da ta sha kashi a wasanni hudu.

Chelsea ta fada wannan halin bayan da a farkon kakar bana masu tsaron bayanta sun sa makulli sun rufe ko ina, amma yanzu sun zama rariya, kuma wadanda suke ci wa kungiyar kwallo kawo yanzu sun kasa tabuka abin azo a gani.

Chelsea ta yi cefanen da ya kai Yuro miliyan 247 fiye da kowacce kungiya a Turai a bana, kuma a lokacin da cutar korona ta nakasa tattalin arzikin kwallon kafa a fadin duniya sai dai hakan yasa har yanzu ‘yan wasan sun kasa tabuka komai.

Cikin fitattun ‘yan kwallon da Chelsea ta dauka sun hada da Kai Habertz kan Yuro miliyan 80 da Timo Werner kan Yuro miliyan 53 da Ben Chilwell kan Yuro miliyan 50 da Hakim Ziyech kan Yuro miliyan 40 da Edouard Mendy kan Yuro miliyan 24 da fitatcen mai tsaron baya, Thiago Silba wanda ya koma kungiyar a kyauta.

Shi dai Habertz ya kasa komawa kan ganiya tun bayan da cutar korana ta damke shi, shi kuwa Werner ya yi wasanni 12 ba tare da ya ci wa Chelsea kwallo ba, karon farko da ya dauki lokaci bai zura kwallo a raga ba tun da ya fara kwallo a kungiyar Stuttgart a kakar wasa ta 2014 zuwa 2015

Tun da aka fara wasannin Premier League na bana, Chelsea ba ta yi nasara a kan manyan kungiyoyin Premier biyar ba da suka hada da yin duro da Manchester United da kuma Tottenham, yayin da Liverpool da Arsenal da kuma Manchester City suka doke ta.

Chelsea za ta fuskanci kalubale nan gaba idan ba ta koma kan ganiya ba, ganin za ta fafata da Atletico Madrid a wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League da za’a koma bugawa a wata mai zuwa.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Dokar Kulle Ba Za Ta Shafi Wasannin Firimiya Ba – Firaministan Ingila

Next Post

Ta Sha Alwashin Cigaba Da Aure-aure Har Sai Ta Samu Mijin Da Suka Dace

RelatedPosts

Diego Costa

Wace Kungiya Ce  Zata Dauki Diego Costa

by Abba Ibrahim Wada
8 hours ago
0

Tun bayan da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, ta...

Zaben Shugaban Barcelona

An Dage Babban Zaben Shugaban Barcelona

by Abba Ibrahim Wada
8 hours ago
0

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bayar da...

ozil

Rikita-Rikitar Da Ta Baibaye Dangantakar Ozil Da Arsenal

by Abba Ibrahim Wada
8 hours ago
0

Kusan yanzu zamu iya cewa ta faru ta kare domin...

Next Post
Aure-aure

Ta Sha Alwashin Cigaba Da Aure-aure Har Sai Ta Samu Mijin Da Suka Dace

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version