Tun bayan kammala zaman aro na shekaru biyu a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, dan wasa Coutinho ya sake komawa uwar kungiyarsa ta Barcelona da buga wasa, wannan koma baya ne ga dan kwallon tawagar Brazil din wanda wasu dalilai suka sa ya kasa taka rawar gani a Barcelona.
Dan kwallon mai shekara 26 a duniya ya koma Camp Nou daga Liberpool a watan Janairun shekara ta 2018 lokacin yana kan ganiyarsa a Liberpool duk da cewa a lokacin itama Liberpool din babu kwararrun ‘yan wasa kamar na yanzu..
Dan wasa ne da Barcelona ta sa ran za ta mora, bayan da Neymar ya koma Paris St Germain da buga wasa kuma a lokacin ne Barcelona ta kwallafa rai cewar Coutinho ne kadai zai iya maye gurbin Neymar din wanda shima dan Brazil ne.
Sai da Barcelona ta biya Liberpool Yuro miliyan 120 da wasu karin tsarabe-tsarabe kafin ya koma Spaniya da buga wasa amma za’a iya cewa ya koma kungiyar ne da kafar hagu domin tun komawarsa abubuwa suka fara lalace masa.
Barcelona da magoya bayan kungiyar sun yi murnar daukar dan kwallon, sai dai kuma Coutinho ya kasa nuna kansa tun lokacin tsohon kociyan kungiyar Ernesto Balberrde daga baya ma ya koma zaman benci.
Coutinho ya kuma je buga wasannin aro a Bayern Munich da yarjejeniyar sayar da shi idan ya taka rawar gani, hakan bai yi wu ba ya koma Camp Nou a kakar bana, bayan da yarjejeniya ta cika.
Dan wasan na tawagar Brazil ya buga wa Barcelona wasanni 14 ya kuma ci kwallo uku a kakar bana sannan ranar 2 ga watan Janairu, likitoci suka yi wa Philippe Coutinho aiki a raunin da ya ji a kafarsa, an kuma dibar masa watanni uku kafin ya koma fagen kwallo.