Kungiyar kwallon kafa ta Burnley ta kawo karshen wasanni 68 da Liverpool da buga filin wasanta wato Anfield ba ayi nasara a kanta ba a wasan da kungiyoyon suka buga ranar Alhamis da daddare.
Wasanni 68 da Liverpool tayi na Premier ba a doke ta ba a Anfield ya zo karshe ne, bayan da Burnley ta doke ta da ci 1-0 a wasansu na daren Alhamis bayan da aka bawa kungiyar ta Burnley bugun fanareti.
Wannan na nufin cewa, tawagar ta Jurgen Klopp sun gaza yin nasara a wasanni biyar da suka buga a jere, lamarin da ke neman ruguza damar kare kabbunsu, ganin cewa ratar maki shida ke tsakanin su da Manchester United dake jan ragamar teburin, a matsayi na hudu.
Rabon Liverpool ta dandana shan kashi a Anfield tun a watan Afrilun shekarar 2017 wanda wannan ba karamin kalubale bane a wajen kociyan kungiyar, Jurgen Klopp wanda yake shan suka bisa halin da kungiyar ta tsinci kanta.
Liverpool – wadda ta dauki kofin gasar Premier a karon farko cikin shekara 30 – tana fuskantar koma baya a wannan kakar wasannin, domin kuwa yanzu tana matsayi na hudu da maki shida tsakaninta da ta daya Manchester United.
Wani koma baya da kungiyar ta fuskanta a wannan kakar shi ne wasanni biyar da ta buga ba ta yi nasara ba, rabon ta da cin wasa tun ranar 19 ga watan Disamba da ta ci kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace daci 7-0.
“Mun sha wuya a wannan wasan, da wahala a fadi yadda aka ji wadannan yaran kamar ba su ba ne suka ci 7-0 a baya, idan muna so mu ci gaba da irin wannan nasarar sai mun kara dagewa amma kuma sun yi kokari a wasan Burnley amma an gaza samun nasara,” in ji Klopp.
Rashin nasarar farko da Liverpool ta yi a gida cikin kwana 1,370 da suka gabata bayan wadda ta yi a hannun Crystal Palace a watan Afrilun shekara ta 2017, amma a wannan karon an doke su bayan da Ashley Barnes ya ci bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Shi ne cinyewa ta farko da aka yi musu cikin wasanni 69, wannan ne dogon lokacin na biyu da wata kungiyar ta dauka ba a doke ta ba a gida, bayan wanda Chelsea ta yi a wasanni 86 kafin a doke ta a watan Oktoban shekara ta 2008.
Duk da cewa suna da masu fama da ciwo kamar Virgil van Dijk da Joe Gomez, amma matsalarsu ta bayyana a cikin filin wasan da suke casa mutane kuma wannan baya rasa nasaba da gajiyar da wasu daga cikin ‘yan wasan sukayi.
Tun lokacin da Sadio Mane ya ci kwallo a wasan West Brom da suka yi 1-1 a ranar 27 ga watan Disamaba, Liverpool ta kai hari 87 a Premier, ciki har da 27 da suka buga a wasan Burnley amma basu zura kwallo a raga ba.