Umar A Hunkuyi" />

Melaye Da Ekweremadu Sun Lashe Kujerunsu

Dino Melaye, ya nana Smart Adeyemi, na Jam’iyyar APC da kasa, inda ya ci gaba da rike kujerarsa ta majalsiar Dattawa.
Jami’in zaben, Emmanuel Bala, ne ya shelanta sakamakon zaben a Lokoja, babban birnin Jihar ta Kogi, da safiyar ranar Litinin. Ya shelanta Melaye, ya sami kuri’u 85,395, inda ya kayar da Adeyemi, wanda ke da kuri’u 66,901.
Melaye ya yi takaran ne a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP. Duk da cewa ya ci zaben a shekarar 2015 a karkashin inuwar Jam’iyyar APC ne, amma sai ya fice ya koma Jam’iyyar PDP a sakamakon rikicin shugabanci da ya mamaye Jam’iyyar ta APC.
Adeyemi, wanda ya ja daga da Melayen a wancan lokacin, ya kuma ja daga da shi a wannan karon amma a karkashin Jam’iyyar APC.
Shi ma mataimakin shugaban Majalisar ta Dattawa, Ike Ekweremadu, ya ci zaben na shi a mazabar Inugu ta Yamma, a karo na biyar a jere.
Da yake bayyana sakamakon zaben a ranar Litinin, Jami’in zaben, Douglas Nwagbo, cewa ya yi, Ekweremadu ya sami kuri’u 86,088 sama da wanda ke biye masa, Juliet Ibekaku-Nwaugwu, ta Jam’iyyar APC, wacce ta sami kuri’u 15,187.

Exit mobile version