Abubakar Abba" />

Mele Kyari Ya Sha Alawashin Sa Ido A Asusun NNPC

Babban Manajin  Darakta na rukunonin kamfanin na NNPC, Mele Kyari ya yi shelar cewa, zai cika alkawarin da kamfanin ya yi na yin aiki da gaskiya ba tare da yin wata badakala ba ko bari a yi.

Kyari ya nuna cewa kwanan nan NNPC za su fitar da cikakken rahoton akawun dinsu, inda ya kara da cewa, wannan ne lokacin da hukumar NEITI ta kai masa wata ziyara.

Babban Manajin  Darakta na rukunonin kamfanin na NNPC, Mele Kyari  ya shedawa  Sakataren na NEITI mai kokarin ganin an yi gaskiya a harkokin man kasar nan, cewa za su fitar da rahoton kudin da su ka kashe abin da an yi shekara da shekaru NNPC ba su yi ba.

Mele Kyari ya nuna cewa ba za su bari wasu su fake da neman bayanai wajen jefa kamfanin cikin rikicin siyasa ba.

A cewar Kyari, ya kamata ku na sane cewa a wasu lokuta a kan samu mutane masu makarkashiya da ke fakewa a karkashin inuwar FOI wajen cin ma manufar siyasarsu, inda ya kara da cewa kamfanin na NNPC na samun wahala da irin wannan.

Babban Manajin  Darakta na rukunonin kamfanin na NNPC, Mele Kyari ya kara da cewa, mu na bi a hankali don kaucewa aukawa a cikin rikita-rikitar rikicin siyasa ko kuma batawa wasu suna.

Shi kuwa Waziri Adio a nasa jawabin ya jinjinawa kokarin da kamfanin na NNPC ke yi a yanzu.

Exit mobile version