Membobin tawagar koli ta JKS sun ziyarci jami’ai da al’ummu mazauna sassa daban daban na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin.
Membobin babbar tawagar da ta gudanar da ziyarar a jiya Alhamis, sun hada da memban zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Wang Huning, da shugaban kwamitin kasa na majalisar bayar da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin.
Tawagar ta ziyarci birnin Korla, inda membobinta suka nazarci yadda ake aiwatar da harkokin raya ilimi da tallafin kiwon lafiya a Xinjiang, da ma yadda ake raya masana’antun dake yankunan karkara, da rayuwa da ayyukan al’umma mazauna yankin.
Har ila yau, yayin ziyarar tasu, Wang Huning ya jaddada muhimmancin bunkasa ilimin bai daya a Xinjiang, musamman a yankin kudanci, tare da kimsa akidar hadin kan dukkanin sassan kasar Sin a zukatan matasa.
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu membobin tawagar sun ziyarci karin biranen yankin da suka hada da Kashgar, da Urumqi, da Karamay, da Bole da kuma Changji. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)