Tare da Dr. Bashir Abusabe
Matakan Gane Adabin Kasuwa abin lura a nan shi ne, irin wannan fasali da Adabin Kasuwar Onisha ya ɗauka shi ne Adabin Elizabeth a Ingila ko kuma na Kitsch a Jamus, da na Larabawa ya ɗauka. Ke nan babban matsugunin kowane aikin adabi da aka yi wa laƙabi da na kasuwa ko na yayi bai wuce irin fasalin da ya tashi da shi ba, ko dai mai arha ne ko kayan da aka yi amfani da su wajen samar da shi ba su da inganci ko kuma masu yin sa da karanta shi wasu gungun jama’a ne, ba na kowa da kowa ba ne. Gungun mutanen na iya kasancewa masu kuɗi ko talakawa ko iyayen gari, sannan uwa uba kuma wannan adabi na da lokacin da yake rayuwa, ya kuma mutu, kamar yadda Malumfashi (2005) ya bayyana.
Domin gane wannan fasali na adabin kasuwa bari mu dubi adabin Elizabeth na Ingila da kyau, ya dai yi tashensa ne cikin shekara 45, wato daga 1558 zuwa 1603, shi kuma na Kitsch da ke a Jamus, ya rayu ne daga 1860 zuwa 1870, wato shekara 10 ya yi a duniya ko kuma na Onisha daga 1947 zuwa 1975, ya shekara 28 ke nan a raye.
Saboda haka, fasalin adabin kasuwa yana zuwa da siffofi da kamannu masu yawa. Sai dai domin taƙaitawa muna iya cewa shi ne adabin da ake samu a cikin kasuwa, ba wai ana nufin kasuwar dole ta kasance irin wadda muke tunani ba, duk inda jama’a suke hada-hadar saye da sayarwa, shi ake nufi da kasuwa a nan. Idan ana son a gane shi da kyau sai a dube shi da waɗannan fasalce-fasalcen : Adabin kasuwa zai iya kasancewa mai saukin karantawa, wato mai jimloli marasa sarkakiya. Haka kuma nahawunsa zai kasance sassauka, ba mai nauyi ba. Haka yawancin wannan adabin yakan kasance bai da yawan shafuka, ma`ana, bai ɗaukar lokaci za a iya karance shi.
Jigogin Adabin Kasuwa
Saƙonni ko kuma jigogin da waɗannan ayyuka na adabi suke isar wa sun bambanta ne daga wannan gari zuwa wancan ko kuma daga wannan kasa zuwa waccan, amma dai abu muhimmi shi ne kowane da abin da yake son ya isar ga al’ummar. Alal misali daga nazarin da aka yi wa Adabin Elizabeth da ya wanzu a zamanin sarauniya Elizabeth ta Ingila a tsakanin ƙarni na 16 da na 17, ya shahara ne ta fuskar wasan kwaikwayo da kuma waƙoƙi, sannan kuma kusan yawancin marubutan suna yin rubutunsu ne domin kare martabar masu mulki da kuma tajirai. Wannan ne ma ya sanya tun daga farkon mulkinta, Sarauniya Elizabeth ta kasance tamkar uwar ƙungiyar, kuma mai ba da taimako ga marubutan, ta yadda kamar yadda muka nuna a wasu lokutta har aiwatar da wasan kwaikwayon ake yi a gabanta.
A adabin Larabawa ma musamman kuwa waƙoƙin lokacin jahiliyya, jigonsu bai wuce faɗakarwa ta zamantakewa ba, ko kuma rayuwa irin ta yau da kullum ba, sai kuma jigon waƙoƙin yawace-yawace da kuma waƙoƙi na ƙabilanci da kusan kowace ƙabila ke da shi. Amma bayan bayyanar Musulunci da wayewar kai sai abin ya canza, domin kuwa litattafan adabin Larabci a lokacin sun fi bayyana rayuwar iyali, misali ayyukan Naguib Mahfuz na Cairo Trilogy, Shi kuwa adabin Onitsha na Nijeriya jigoginsu sai suka sha bamban da na sauran sassan duniya, domin kuwa a lokacin da aka fara samar da shi a 1947, sai ya kasance ya ta’allaƙa ne wajen ba da labaran soyayya da suka shafi aure da kuma kasuwanci, a sassan wannan yanki na Nijeriya. Ke nan, ana iya cewa yawancin labaran na Adabin Onisha ba su maganar komai sai labaran soyayya da tatsuniyoyi. Daga baya kuma sun tattauna abubuwa da suka shafi yadda ake rubuta wasika da yadda ake koyon Ingilishi da kuma tallata haja da makamantansu.
Daga binciken da aka gudanar an dai fahimci cewa yawancin jigogi na yawancin Adubban Kasuwa a kowace kasa, suna kasancewa abin da al’ummar wannan wuri ne suka fi so da ko sha’awar gani ko karantawa a daidai lokacin da ake aiwatar shi, ko dai na soyayyar ne ko kuma na kasuwanci, ko rayuwar iyali ko kuma na masu mulkin, kusan a ce wannan shi ya fi rinjayar masu karanta ko sauraron wannan adabi na wannan yanki.