Tare da Dr. Bashir Abusabe
Masu Sayarwa
Kamar kowane irin tsarin adabin kasuwa, Adabin Kasuwar Kano ya zo da nasa fasalin sayar da littattafan. Sai dai shi ma kamar sauran a na sayar da littatafan ne a manyan kasuwannin ƙasar Hausa da suka haɗa da Kano da Kaduna da Jos da Sakkwato da Zaria da Gusau da Gombe da Bauchi da Minna da Katsina da sauransu da dama.
Waɗanda suka taimaka a wannan fage kamar yadda Adamu (2002) ya bayyana su ne dillalai ko masu bugawa da sayarwa a kasuwannin Kano da sauran sassan ƙasar Hausa, musamman da yake a wancan lokaci ba wani shago da ake da shi da ke tallata littatafan Hausa kurum. A birnin Kano, inda nan ne harkar ta zaunu sosai akwai irin su Alhaji Baba, mai Jakara City Bookshop da Alhaji Musa Ɗanbala, mai Sauki Bookshop da Alhaji Garba Mohammed, mai Garba Mohammed Bookshop.
Haka wannan harkar ta ci gaba da wanzuwa har ta kai an samar da shaguna da suke ba sayarwa kurum suke yi ba suna bayar da hayar waɗannan littatafai ga waɗanda ba su da ƙarfin sayen littattafan ko kuma ba su son su tara su jibgi a gida.
Masu Karatu
Masu karatun waɗnnan litattafan kamar yadda muka gani a can baya mafi yawa matasa ne. Sai dai domin mu fahimci inda aka fito dangane da wannan ɓangare na bincike, na ga ya dace a bi diddigin game tunanin masu karanta waɗannan littatafai. Hanyar da aka bi domin yin haka, ita ce ta rarraba takardun neman bayanai domin a ji daga bakin masu karatu game da abubuwa da dama da suka shafi wannan harka. Daga cikin takardun neman bayanai sama da 400 da aka rarraba a sassan garuruwan ƙasar Hausa, kamar Katsina da Kano da Kaduna da Sakkwato da Zariya da Gombe da Dutse da kuma Bauchi, an samu guda 350 da suka dawo hannu. An yi amfani da waɗannan takardun bayanai domin gane matsayin makaranta wadannan littattafai. Ga dai fasalin rabe-raben takardun neman bayanin da aka samu.