Mene Ne Ainihin Nufin Amurka Kan Philippines?
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mene Ne Ainihin Nufin Amurka Kan Philippines?

byCGTN Hausa
2 years ago
Amurka

Jiya Talata ne Gina Raimondo, ministar kasuwanci ta kasar Amurka ta bayyana a birnin Manila, fadar mulkin kasar Philippines cewa, Amurka za ta goyi bayan Philippines wajen ninka yawan masana’antun kera sassan na’urorin laturoni na semiconductor, a kokarin magance samun yawan masana’antun kera mattarar bayanai ta microchip a wasu sassan duniya. Kafin wannan kuma, ta sanar da cewa Amurka za ta zuba jarin dalar Amurka fiye da biliyan 1 a Philippines. Shin Amurka tana son taimakawa Philippines ne cikin sahihanci? Ko kuma ta tsara nata makarkashiya?

A shekarun baya-bayan nan, Amurka ba ta zuba jari da yawa a Philippines ba, inda ta kan zuba mata dalar Amurka biliyan 1 a ko wace shekara. Tun bayan kafuwar sabuwar gwamnatin Philippines a watan Yunin shekarar 2022 har zuwa yanzu, Amurka ta kara hada hannu da Philippines, a yunkurin aiwatar da manyan tsare-tsare a yankin tekun Indiya da Pasific. Amma ba ta kara zuba jari a Philippines ba. Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2023 da ta gabata, Amurka ta kasance kasa ta 6 a fannin zuba wa Philippines jari, tare da zuba mata dalar Amurka biliyan 1, yayin da Amurka ta zuba wa Thailand dalar Amurka biliyan 2.3. Abin da ya kamata a lura shi ne jimillar mutanen Philippines ta fi ta Thailand yawa har da miliyan 40.

  • Dokar Hana Sayar Da Burodi Mara Shaida, Litar Mai Fiye Da 50 Ta Tabbata A Zamfara, Gwamna Dauda Ya Sa Hannu
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 10 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Zamfara

A matsayin kasar da ba ta cikin nahiyar Asiya, Amurka tana son kara hada hannu da Philippines ne domin yin amfani da ita wajen yaki da kasar Sin da kuma takaita karfin kasar Sin. Alal misali, Amurka ta riga ta sa hannu sosai cikin batun tekun kudancin kasar Sin.

A bangaren Philippines kuma, shin ba ta san ainihin manufar Amurka ba ne? A’a, ta sani sarai, tana son yin amfani da karfin Amurka domin cimma burinta, wato hawan dutsen teku na Ren’ai Jiao da tsibirin Huangyan a kullum, da samun riba sakamakon yadda Amurka ta danne ci gaban kasar Sin ta fuskar mattarar bayanai ta microchip. Amma a karshe dai za ta rasa abin da ma can ba nata ba ne. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1

SAHUR [Falalarsa Da Fa'idojinsa] Na 3

LABARAI MASU NASABA

…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version