Mene Ne Laifin IPOB Idan Ta Bukaci Shugaban Tsaro Ya Kasance Ibo? – Gwamnan Abiya

IPOB

Daga Yusuf Shu’abu,

Gwamnan Jihar Abiya, Okezie Ikpeazu ya bukaci gwamnatin tarayya ta bude kofar tattaunawa da haramtacciyar kungiyar da ke neman kasar Biyafara (IPOB), kamar yadda aka tattauna da sauran irin wadannan kungiyoyi a cikin kasar nan, a matsayin wata hanyar dakile rashin tsaro a Nijeriya.

Ana ci gaba da kai hare-hare a jihohi biyar da suka hada da Inugu da Ebonyi da Anambra da Imo da Abiya da ke yankin Kodu-maso-Gabas. Ana yawan banka wa kotuna da ofishoshin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) wuta a wadannan yankuna.

Mista Ikpeazu ya bayyana cewa, wannan farmaki ne na ta’addanci wanda ake tsorata ‘yan sanda domin su kasa gudanar da ayyukansu da ya rataya a wuyansu. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani hira da gidan talabijin din Channels ya yi da shi a cikin shirin siyasa a yau. Mista Ikpeazu bai natsu da ayyukan da kungiyar IPOB ke gudanarwa a cikin jiharsa. Ya siffanta kungiyar da kokarin cika gurbi bisa kuskure tare da kara fadada ayyukanta na ta’addanci a yankunan Kudu-maso-Gabas.

“Tun farko mene ne mafarin kawo tashin hankali a yankin Kudu-maso-Gabas. Wasu daga cikin mutanen yankin Kudu-maso-Gas ba sa samun kariya bisa yadda abubuwa suke faruwa na ta’addanci da ake samu a dazukanmu.

“An yi wa yankin nisa wanda a yanzu haka mahukunta ke kokarin cikewa,” in ji gwamnan.

Da aka tambaye shi a kan umurnin da kungiyar ta bayar na zaman gida, ya ce, “akwai matsaloli a cikin wannan lamari, mutane da dama suna bukatar gudanar da wasu abubuwa kamar na tsare gonaki da tsare mutane a cikin dazuka, idan jami’an tsaro suka gaza yin haka, to mutane za su nemi taimako ta kowani yanayi.

“Yana da kyau a saurari korafinsu, saboda mafi yawanci abubuwan da suke bukata akwai wadanda talakawan yankin ne ke bukata. Mene ne kuskuren sauraransu?

“Mene ne laifin kungiyar IPOB  idan ta bukaci shugaban tsaro ya kasance Ibo, me zai hana faruwar hakan?”

Ya kara da cewa, ya kamata gwamnatin Nijeriya ta tattauna da su cikin gaggawa.

An tambayi Mista Ikpeazu ko ya taba kokarin tattaunawa da kungiyar.

“Zai yi wa mutum daya wahala ya iya yin hakan, domin sai gwamnatin tarayya,” in ji gwamna.

A kan batun umurnin kungiyar IPOB, gwamnan ya bayyana cewa ya rage wa mazauna yankin su bi wannan umurni ko kuma kar su bi.

“Idan mutane suka yanke shawarar ba za su je kasuwa ba ko wuraren kasuwancinsu, gwamnati ba ta da hurimin takura musu a kan dole sai sun je kasuwa.”

Mista Ikpeazu ya ci gaba da cewa, gwamnonin yankin suna iya bakin kokarinsu na tsare mazauna yankin. Ya ce, Jihar Abiya tana da kungiyar sa-kai da ke yaki da rashin tsaro a jihar.

Exit mobile version