Mene Ne Tsarin Manhajar Android (Android system)?

Tare da Bakir Muhammad

Android kamar yadda kowa ya sani wata nau’in tsarin manhajar waya ce da ke kishiyantar manhajar iOS da ta Blackberry, kamfanin Google ne suka kirkire wannan tsarin manhajar ta Android, kuma ta na amfani da wata fasaha ne mai suna Linud Kernel wacce aka yi ta musamman don manyan wayoyin hannu wanda ba sa amfani da madannai, amma an fadada fasahar yanzu akwai talbijan, da motar hawa, da agogon hannu da kyamara duk masu amfani da tsarin Android.

A shekarar 2005 aka kammala tsarin manhajar ta Android amma ba’a kaddamar da shi ba sai a shekarar 2007, an kaddamar ne tare da manhajar da ta dace da ta tsarin Android (Applications) da kuma bangarorin da su ma za su dace da tsarin manhajar (Hardware) misali lasifika, da wajen Magana (Microphone) ga gilishin gaban waya (Touchscreen) da sauran su masu yawa, a shekarar 2008 aka kaddamar da wayar hannu mai amfani da tsarin Android ta farko.

Andy Rubin da Rich Miner ne suka kirkiro wannan tsarin manhajar a Palo Alto da ke garin California na kasar Amurka, sun kirkiro wannan tsarin manhajar ne domin ciyar da amfani da wayoyin hannu gaba, tsari ne da zai taimaka matuka wajen sannin ainihin inda wanda yake amfani da wayar yake, da kuma sannin me ya fi bukata,a lokacin babu manyan wayoyi sai wadanda suke amfani da tsarin manhajar Symbian da Microsoft window kadai, su kuma basa wadatar ba wajen wasu abubuwan.

Wayoyin da suka fara fitowa da wannan tsarin manhajar android sune HTC kamfanin kasar Taiwan, Motorola da Samsung, wayoyin da suka fitowa da tsarin manhajar mafi ywansu sunyi kama da wayoyin Blackberry wato basu da gilashin tabawa (Touchscreen) sai madannai kawai, amma fitowar wayar iPhone mai amfani da tsarin manhajar iOS ta farko wacce ba ta da madannai ya sa aka canza yanayin Android daga wacce take da madannai zuwa wacce ba ta da madannai sai gilashin tabawa kawai.

Wayoyi da suka fara fitowa suna da tsarin manhajja nau’i daban daban, misali akwai “Cupcake” da “Donut” da “Éclair” da kuma “Froyo”, a shekarar 2013 yayin kaddamar da tsarin manhajja nau’in “KitKat” kamfanin ya sanar da tsarin sanya suna na nau’in tsarin manhajojin wayar, y ace daga lokacin za su dinga sama mu su sunaye irin sunayen abubuwan kwalam da makwalashe (Desserts), sanadiyar jin dadi da wayoyin suke kawo ma rayuwar masu amfani da su.

Wayoyin masu amfani da tsarin manhajar Android sun fi sauran kishiyoyin su saukin amfani, sunfi arha ma a kasuwa, sannan manhajjojin (Apps) da masu amfani da wayoyin su ke bukatar amfani da su suna da saukin samuwa, a na iya samun su a kantin manhajjoji na “Google Store” da yak e zuwa a kan ko wacce wayar Android, da yake wayoyin da batir su ke amfani, duk lokacin da ba a amfani da wata manhajja to wayar da kan ta za ta kulle wannan manhajar saboda ta rage shan batir, sannan kayayakin wayar Android suna da saukin mu’amala, ta yadda ba za a sha wahala ba wajen gyara su in sun samu matsala.

A halin yanzu duk da matsalar tsaro da masana suka ce wayoyin na android suke da shi mafi yawan mutanen duniya da suke amfani da manyan wayoyin hannu da Android suke amfani, akwai kamfanoni sama da hamsin da suke kera wayoyin android, sannan ko wanne kamfani ya na da nau’ikan wayoyin akalla sama da goma, sannan akwai kamfanoni da ba su tsaya a wayoyin hannu ba kawai, akwai Talbijan mai dauke da tsarin manhajar android, akwai agogon hannu ma, ga kuma motoci masu sarrafa kansu duk suna dauke da tsarin manhajar ta Android.

Exit mobile version