Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
Batun Dimokradiyya shi ne lamarin da ahalin yanzu ke kara dumama yanayin harkokin yau da kulllum, musamman ganin yadda duniya ke kara daukar sabbin salon komawa tsarin Dimokradiyyar da tuni kasashen yamma suka jima da fara amfanar da al’ummarsu romon Dimokradiyya.
Amma idan ka dawo kasashe irin namu na Afirika musamman ma a nan Nijeriya, har yanzu batun demakaradiyya tatata yake, bai kai ga fara tsayawa da kafarsa ba. Wannan kuma kila baya rasa nasaba da halayyar wadanda ke sahun gaba cikin harkokin jan ragamar Dimokradiyyar tamu.
A jiha irin ta Kano wadda ke sahun gaba wajen yaye fitattun ‘yan siyasar da ake alfahari da nagartarsu, da kuma kokarin samar da dondamalin da talakawa za su fara aminta da cewar don su ake komai idon ana maganar ci gaban al’umma, haka kuma ire-iren wadancan zaratan mutanen da jihar Kano ta samar su ne ke zaman mudubin dubawa ga duk wani wanda ke son zama wani abu ta fuskar siyasa.
Lokaci ya yi da ya kamata matasa su farka daga dogon barcin da ke neman wuce gona da iri, musamman ganin yadda a Jihar Kano a kullum abin da ‘yan siyasa ke nunawa shi ne matasa sune jigon al’umma, kuma su ake fatan samarwa makoma tagari. Amma babban abin taikaci shi ne matasan sun zama‘yan turin mota, da idan ta shi sai a tule su da hayaki a wuce, sai kuma kakar zabe ta sake zagowa. Hakan ta sa a lokacin irin wannan ganin haskawa matasan da aka hanken za su yi amfani da shekarunsu wajen yayyafa wa matasa ruwan sanyin da kila su farka daga dogon barci da suka shafe shekaru suna yi.
Alhaji Ibrahim Al’amin (Little) matashi ne wanda kuma a kullum matasan suka amince da cewar matukar ya samu damar jagoranci babu shakka Allah zai tarfa wa garin matasa nono, idan za a iya tunawa Ibrahim Al’amin ya taba fitowa takarar Gwamna a karkashin tutar Jam’iyyar APP, wanda shi ne ya lashe zaben fidda gwani, amma daga baya aka ce yana da matsala aka karbe takarar aka baiwa Malam Ibrahim Shekarau, wanda bayan an kara zaben da Jam’iyyar PDP ya lashe zabe.
Dagan an Ibrahim Al-amin ya koma jam’iyyar PRP inda ya yi takarar Gwamnan da bai samu Nasara a wancan lokacin ba. Ganin irin salon yakin neman zabensa wanda matasa maza da mata suka sadaukar da duk abin da suke dashi wajen dafawa takarar tasa, ya sa kodayaushe ba wanda matasa ke kwadayin zama gwamnan Kano kamar Ibrahim Al’amin.
Gogaggen dan Kasuwa masanin ilimin kwamfyuta ya goge wajen sanin siddabarun yadda za a samarwa matasa hanyoyin dogaro da kai, sanann kuma duk inda ya shiga walau ta fuskar siyasa ko aiki, babban abin da yafi zuwa zuciyarsa shi ne me za ayi matasa su dai na walagigi kuma adaina amfani dasu wajen jagaliyar siyasar da ako da yaushe kura da shan duka gardi da kwashe kudi. Yakware tare da samun tarbiyyar girmama na gaba da kuma mutunta Jam’iyya da biyayya ga wadanda Allah ya damka amanar jagoranci a hannunsu, wannan ta bashi damar mallakar zukatan manya da yara, maza da mata.
Yanzu haka Ibrahim Al-amin ya koma jam’iyyar PDP wadda ake ganin bakaramar Nasara Jam’iyyar ta yi ba wajen karbar jarumi kuma dan kishin ci gaban al’umma, hakan ta sa yanzu gamayyar kungiyoyi suka fara kiran shi da ya fito takarar Gwamnan Kano akakar zabe mai zuwa na shekara ta 2019, har ma aka fara jin wasu hamshakan ‘yan siyasa irinsu Alhaji Bala Baico wanda ya taba zama wakili a majalisar wakilai ta tarayya na tabbatar da aniyarsu ta ci gaba kiran matashi domin amsa kiran matasan jihar Kano don shiga takarar gwamna a Kano. Wasu ma na cewa idan Ibrahim Little ya nuna kin amincewa da wannan bukata ta matasan kila su gurfanar da gaban kuliya, domin shi ne kadai ya rage damar da matasa ke da ita na wanda ya san darajarsu kuma ake hangen kyakkyawar makoma ga matasan idan Allah ya ba shi mulkin Kano. Har yanzu dai matashin dan siyasar Alhaji Ibrahim Al-amin ba aji daga bakinsa ba cewar zai shiga wannan takara ko a’a, lokaci kadai zai tabbatar da hakan, amma dai yanzu haka akwai sama da kungiyoyi hamsin da suke neman amincewarsa domin yin takarar a Kano.