Kungiyar kwallon kafa ta Santos dake kasar Brazil, wato kungiyar da shahararren dan wasan Brazil Pele ya bugawa wasa a lokacin da yake matashi ta karyata zancen da akeyi na cewa dan wasa Lionel Messi ya karya tarihin dan wasa Pele wajen cin kwallaye a kungiya daya.
A satin daya wuce ne dan wasan tawagar Argentina Lionel Messi, ya kamo tarihin da tsohon dan wasan Brazil, Pele, ya kafa na cin kwallaye 643 a kungiya daya, bayan kwallon da ya ci wa kungiyarsa ta Barcelona a wasan da ta buga da Valencia sannan ya sake zura kwallo daya wadda tasa ya zarta Pele din a wasan da suka fafata da Valladolid a ranar alatar data wuce.
Sai dai a wata sanarwa da kungiyar Santos ta fitar a shafinta na Internet, kungiyar tace Pele kwallae 1091 ya zura a raga kuma a cikin kwallayen babu wadanda ya zura a wasannin biki ko kuma na sada zumunci.
Santos ta ci gaba da cewa ana kokarin ragewa Pepe kwallaye 448 a cikin kwallayensa kuma a cikin kwallayen da ake son ragewa akwai kwallayen daya zura akan manya-manyan kungiyoyi a duniya ciki har da Inter Milan wadda take babbar kungiya a shekarar 1960.
Santos ta kara da cewa duka wasannin da Pele ya buga sun samu sahalewar hukumar kwallon kafa ta Brazil ko kuma ta yankin kudancin Amurka saboda haka wasannin da akace babu su a lissafi hukumomi ne suka amince ayi wasan saboda haka dole ne ayi lissafi dasu.
Messi ya buga wa Barcelona da ke Sifaniya wasanni a kakar wasa har 17 da ya yi, tun bayan fara wasansa a shekarar 2004 kuma gwarzon dan wasan Brazil ya fi kowa yawan cin kwallaye a kungiyar Santos a kakanni 19 da ya buga da kungiyar.
Har ila yau Messi na cikin manyan ‘yan wasan duniya da suke haskakawa sama da shekara 10 a jere, tare da takwaransa na Juventus Cristiano Ronaldo wadanda cikin shekaru goma na baya suka mamaye kwallon kwafa ta hanyar lashe kowacce irin kyauta ta nuna bajinta.
Sai dai a wannan kakar Messi na fuskantar koma baya na rashin kokarin kungiyarsa ta Barcelona wadanda wasu ke dora alhakin hakan a kan shi duk da cewa a kwanakin baya ya bayyana cewa yana son barin kungiyar
Hakan na da alaka da rikicin da ya fuskanta a baya da kungiyar kan cewa sai ya sauya sheka, inda La Liga da Barcelona suka sanya sharudan abin da za a biya kafin tafiyarsa matakin da aka kasa samun kungiyar da zata iya biyan kudin..
Sharadin kuwa shi ne dole duk kungiyar da ke son sayensa ta biya yuro miliyan 700 kudin darajar dan wasan kuma mafi yawan kungiyoyi sun ce ba za su iya cika sharadin ba lamarin da ya sa Messi ya fasa barin kungiyar a watan Agustan da ya wuce.