Dan wasan kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo ne ya lashe kyautar ta zakaran kwallon kafa na turai a shekarar 2016, yayin da dan wasan kungiyar Barcelona Lionel Messi ya kalubalanci shi, da kuma mai tsoron gida na kungiyar Juventus wato Buffon.
A bana ma an sake sanya sunayen, Gianluigi Buffon, Lionel Messi, da kuma Cristiano Ronaldo a jerin sunayen yan takarar zakarun na turai UEFA.
Kyautar da aka fisani da sunan ‘dan wasan da yafi iya taka leda’ Ronaldo ne ya cinye kyautar a shekarar da ta gabata, shi kuma Messi ya lashe kyautar har sau biyu, a yayin da Iniesta da dan wasa Frank Ribery suka lashe sau daya.
Hukumar kwallon kafa ta FIFA na zabar ‘yan wasa ne da suke buga kwallo a turai ba tare da la’akari da kasar da suka fito ba, alkalai 80 ne suke zabar mutum uku daga kungiyoyin wasan da suke taka leda a turai.