Messi Da Ronaldo Sun Nuna Bajinta A Kofin Zakarun Turai

Messi

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German Lionel Messi ya ci wa kungiyar ta Paris St-Germain kwallo biyu a karawar da ta doke RB Leipzig 3-2 a Champions League ranar Talata.

Dan wasa Kylian Mbappe ne ya fara ci wa PSG kwallo a wasa na uku-uku na cikin rukuni da suka kara a Faransa, sai dai kuma Andre Silba ne ya farke kwallon, sannan Nordi Mukiele ya kara ta biyu da kungiyar Jamus ta shiga gaba.

Daga baya ne Messi ya farke wa PSG, sannan ya ci ta uku a bugun fenariti kuma PSG din ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga dab da za’a tashi, maimakon Messi ya karbi kwallon ya buga, sai Mbappe ne ya karba ya buga kwallo ya yi sama.

Kungiyar Faransa tana saman Manchester City a rukunin farko da maki bakwai a Champions League, sannan kawo yanzu Messi ya ci kwallo uku a PSG a Champions League, tun bayan da ya koma kungiyar, wanda ya ci daya a wasan da suka doke Manchester City 2-0.

Messi tsohon dan kwallon Barcelona kawo yanzu ya ci kwallo 123 a gasar Zakarun Turai kenan da 120 da ya zura a raga a Barcelona, kuma Leipzig ita ce ta 37 da ya ci a Champions League.

Kyaftin din na Argentina ya zama na hudu da ya zura kwallo a wasa biyu a jere a PSG da komawarsa kungiyar da buga wasa, bayan Neymar da Aled da kuma George Weah wadanda suka yi irin wannan bajintar a baya.

Kawo yanzu Leipzig ta yi rashin nasara a wasanni uku a ‘Champions League’ a bana, kuma wasa hudu ta ci a bana a dukkan fafatawa tun bayan da Jesse Marsch ya karbi aikin horar da kungiyar.

A kasar Ingila kuma kungiyar Manchester United ta sha da kyar a hannun kungiyar Atalanta ta kasar Italiya a wasa na uku-uku na cikin rukuni na shida da suka fafata a Champions League ranar Laraba.

Manchester United din ta yi nasara a kan kungiyar Italiya da ci 3-2 da hakan ya bai wa kungiyar Ingilan damar hawa kan teburi na shida da maki shida kuma Atalanta ce ta fara cin kwallo ta hannun Mario Pasalic a minti na 15 da fara wasa, sannan Merih Demiral ya kara ta biyu a minti na 29.

Daga nan ne aka yi hutu, an ci Manchester United 2-0 a katafaren filin wasa na Old Trafford, inda ‘yan kallo suka yi wa kungiyar ihu kan kasa sa kaimi a fafatawar, sai dai bayan da aka koma zagaye na biyu ne dan wasa Marcus Rashford ya farke daya, sannan Harry Maguire ya zare ta biyu, sai Cristiano Ronaldo da ya ci ta uku saura minti tara a tashi daga wasan.

Ronaldo ya ci kwallo uku a wasa uku a jere a Champions League a Manchester United karo na biyu da ya yi wannan bajintar, bayan cikin Nuwambar 2007 a kakar da ya lashe kofin a kungiyar.

Da wannan sakamakon Manchester United ta koma ta daya a kan teburi na shida da maki shida, ita kuwa Atalanta ta koma ta biyu da maki hudu, ya yin da Billareal ta koma ta uku da maki hudu, bayan da ta ci Young Boys 4-1.

Matashin dan wasa Amad Diallo bai murmure ba, domin fuskantar tsohuwar kungiyarsa mai shekara 19 dan kasar Ibory Coast bai buga wasa ko daya ba a kakar nan kuma wannan shi ne karon farko da kungiyoyin biyu suka kece raini a tsakaninsu.

Dukan sakamakon wasannin Champions League da aka buga ranar Laraba:

Barcelona 1-0 Dinamo Kieb – Red Bull Salzburg3-1 Wolfsburg – Chelsea 4-0 Malmo – Manchester United 3-2 Atalanta – Lille 0-0 Sebilla – Young Boys 1-4 Billarreal – Benfica 0-4 Bayern Munich – Zenit St. Petersburg 0-1 Juventus.

Exit mobile version