Abba Ibrahim Wada" />

Messi Da Ronaldo Sun Yi Min Nisa A Kwallon Kafa, Cewar Muhammad Salah

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Muhammad Salah, dan kasar Masar, ya bayyana cewa shahararrun ‘yan wasannan guda biyu, Messi da Ronaldo sunyi masa nisan da bazai iya kamo suba

A cikin satin daya gabata ne tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya ce har yanzu Muhammad Salah na Masar da ke buga wasa a Liverpool na da cikakkiyar damar kamo takwarorinsa Cristiano Ronaldo na Juventus da kuma Lionel Messi na Barcelona, matukar ya cire son rai ya kuma ci gaba da zura kwallo kamar yadda ya faro a kakarsa ta farko da zuwa Liverpool.

Wenger a zantawarsa da wata jaridar wasanni, ya ce babu shakka kwazon dan wasan ya yi kasa bayan da ya fara nuna son kai wajen ganin lallai duk kwallon da ya kakko shi zai kai ta raga, wanda kuma a cewar tsohon kocin hakan na matsayin koma baya ga ‘yan wasa.

Wenger ya gwada misali da sabanin da ya faru tsakanin Salah da Mane a makon jiya, yayin wasan da suka lallasa Burnley da kwallaye 3 da 1 inda Salah yaki bai wa Mane kwallo don ya zura a raga matakin da ya harzuka Mane.

“Ronaldo da Messi ‘yan wasane wadanda suka dade suna buga wasa a matakin manyan ‘yan kwallo kuma har yanzu tauraruwarsu tana haskawa a duniya saboda haka har yanzu ban kai matsayinsu ba kuma sunyi min nisan da bazan iya kamo suba’ in ji Salah

Arsene Wenger wanda yanzu haka ya ke zaune ba tare da aikin yi ba, tun bayan ajje aikin horar da Arsenal bara bayan shafe shekaru 22 a waje guda, ya ce dole ne Salah ya kwaikwayi takwarorinsa Ronaldo da Messi wajen sanin lokacin da ya dace ya zura kwallo da kuma lokacin da ya kamata ya bayar da dama ga wasu su zura don ci gaban kungiyar da yake, ko da dai ya ce shima Mane da Firmino dole sai sun sadaukar da wasu burukansu ta hanyar bayar da cikakkiyar dama ga Salah kamar dai yadda Suarez da Neymar suka yiwa Lionel Messi a Barcelona da yadda Benzema da Bale suka yiwa Ronaldo lokacin da yana Real Madrid.

Exit mobile version