Connect with us

WASANNI

Messi Daga Wata Duniyar Ya Zo, Cewar Mai Koyar Da Barcelona

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Barcelona Enesto Balberde ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, Leonel Messi daga wata duniyar ya zo, duba da irin yadda yake zura kwallaye a raga babu kakkautawa.

Lionel Messi na Barcelona ya fara gasar zakarun Turan bana da cikakken karsashi, lura da kwallaye uku da ya zazzaga a wasan da suka lallasa PSB Eindhoben da ci 4-0 a ranar Talata.

Bayan jefa kwallon ta uku, abokan wasansa sun rufe shi saboda murna, yayin da magoya bayansa suka yi ta wake-waken kiran sunansa, in da kuma kocinsa, ya bayyana shi a matsayin wani abu da ba a taba gani cikin tsawon shekaru ba.

A karo na takwas kenan da Messi ke zura kwallaye uku-uku a wasannin zakarun Turai, in da ya zarce babban abokin hamayyarsa na Jubentus Christiano Ronaldo, wanda ya zura kwallaye uku-uku har sau bakwai a wasannin na gasar zakarun Turai.

Idan za a iya tunawa, Messi ya gaza kai tawagar kasarsa ta Argentina ga gaci a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Rasha. Haka zalika Roma ta yi waje da su a gasar zakarun Turai a bara, abin da bisa dukkan alamu ya bakanta ran gwarzon dan wasan, musamman idan aka yi la’akari da jawabin da ya yi wa magoya bayansa a Camp Nou.

“Messi daga wata duniyar yake domin yana yin abubuwa ba kamar yadda kowanne dan kwallo yake yi ba sai dai muce mu anan Barcelona munyi nasarar samun dan wasa kamarsa” in ji kociyan kungiyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: