Abba Ibrahim Wada" />

Messi Na Dab Da Karya Tarihin Pele

BARCELONA, April 17, 2019 (Xinhua) -- FC Barcelona's Lionel Messi celebrates during the UEFA Champions League quarterfinal second leg soccer match between FC Barcelona and Manchester United in Barcelona, Spain, on April 16, 2019. Barcelona won 3-0 and entered the semifinal with a total score of 4-0. (Xinhua/Joan Gosa/IANS)

Hamshakin tauraron dan wasa Lionel Messi na kan hanyar karya tarihin da a ka yi imanin cewa ba zai karyu ba na kwallo 643 da shahararren dan wasan Brazil Pelé ya ci wa kungiyar Santos ta Brazil din a tsawon shekara 18 da ya yi ya na buga wasa.
Yanzu haka saura kwallo 39 Messi ya kamo waccan lamba da Pele ya gindaya kuma kwallon da Messi ya ci a wasansu da Sebilla a daren Lahadi  ta farko kenan a La Ligar bana kuma ita ce ta 604 a Barcelona.
Ganin cewa ya ci wa Barcelona kwallo sama da 40 a kowacce kakar wasa 10 da ya buga, Messi mai shekara 32 a shirye ya ke tsaf ya karya alkadarin Pele a kakar bana sai dai kafin zuwan Messi harkar kwallon kafa ba a taba tsammanin akwai wanda zai kamo Pele ba a tarihin da ya kafa a shekarun 1956 zuwa 1974.
Dan wasan Bayern Munich Gerd Müller ne kadai ya kusa kai wa ga gaci, inda ya ci wa Bayern Munchen din kwallaye 565 daga shekarar 1964 zuwa 1979 sai dai shi ma daga baya ya kasa saboda yanayin ciwon da ya yi fama da shi.
Tun bayan da ya saka rigar Barcelona a shekarar 2004, Messi ya zura kwallo 420 a La Liga, 112 a kofin zakarun turai na Champions League, sai guda 51 a Copa del Rey, guda 13 a Spanish Super Cup, guda biyar a Club World Cup sai kuma kwallaye uku a UEFA Super Cup.
Sai dai tuni masana tarihin kwallon kafa su ka bayyana cewa wannan tarihin da Messi ya ke kokarin karyawa babu makawa zai karya shi duba da irin tasirin da dan wasan ya ke da shi har yanzu a kwallon kafa.

Exit mobile version