Messi Ne Ya Lashe Kyautar Takalmin Zinaren Gasar Zakarun Turai

Kaftin din kungiyar Barcelona Lionel Messi, ya lashe kyautar takalmin zinare na gasar zakarun Turai ta bana, bayan nasarar zama dan wasan da ke gaba wajen yawan kwallaye a gasar. Messi dai na da kwallaye 12 a gasar ta bana, yayin da dan wasan gaba na Bayern Munich Robert Lewandowski ke biye masa a matsayi na 2 da kwallaye 8.

Sergio Aguero na Manchester City, Moussa Marega na FC Porto, Dusan Tadic na Ajax da kuma Crsitiano Ronaldo na Juventus, dukkanin su na da kwallaye 6, a matsayi na uku.

Sauran ‘yan wasan da ke biye wajen yawan kwallayen da suka ci wa kungiyoyinsu, sun hada da Lucas na Tottenham, Neymar na PSG, Sterling na Manchester City, da Muhammad Salah na Liverpool, sai kuma Dybala da Harry Kane na kungiyar Tottenham, wadanda kuma dukkaninsu ke da kwallaye 5.

Exit mobile version