A ranar Asabar Barcelona ta ci Espanyol 5-0 a gasar La Liga wasan mako na uku da suka kara a Camp Nou.
A karawar ce Lionel Messi ya ci kwallo uku rigis, kuma karo na 38 kenan yana yin haka tun komawarsa Barcelona da taka-leda a matsayin kwararren dan kwallo.
Jumulla ya ci kwallo uku sau 27 a gasar La Liga da kuma sau bakwai a gasar cin kofin zakarun Turai da sau uku a Copa del Rey da sau daya a Spanish Super Cup.
Karo na uku kenan Messi dan kasar Argentina yana cin Espanyol kwallaye uku a wasa, amma Balencia ce kungiyar da ya fi cin kwallo uku rigis, wacce ya yi wa hakan sau hudu a tarihi.