Connect with us

WASANNI

Messi Ya Nemi A Yi Afuwa Ga Wanda Ya Shiga Fili

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kuma kyaftin din kungiyar, Leonel Messi, ya nemi a yi wa magoyin bayan kungiyar ta Barcelona wanda ya shiga filin wasa a guje, domin ya yi hoto da zakaran na duniya afuwa.

A wasan dai Barcelona ta buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Real Mallorca ne dai wani magoyin bayan kungiyar yah aura cikin filin wasan ba tare da sanin jami’an tsaro ba inda ya je, domin daukar hoto da Messi.
Sai dai tuni mahukuntan gasar La Liga su ka ce za su dauki mataki na shari’a kan wanda ya shiga fili zai dauki hoto tare da Messin a ranar Asabar din data gabata saboda yadda a ka hana cakuduwa cikin mutane saboda tsoron yada cutar Korona.
Sai dai bayan da dan wasa Messi yaji labarin abinda yafaru da kuma irin hukuncin da hukumomi suka shirya za su yi akan magoyin bayan shine ya fito yana neman afuwa kuma yana fatan hakan ba za ta sake faruwa ba.
“Ina neman afuwa akan abinda ya faru tsakanina da magoyin baya tabbas yayi kuskure idan muka duba yadda hukumomi suka kaffa-kaffa da lafiyar duk wani dan kasa sai dai wannan ya karya doka amma duk da haka ina nema masa afuwa” in ji Messi.
Ya ci gaba da cewa “Tabbas yayi babban kuskure kuma laifine babban amma ganin halin da ake ciki yana fatan za a yi masa afuwa sannan a gargade shi akan sake aikata irin wannan laifin a nan gaba musamman a wannan lokacin da duniya take fama da annoba”
Mutumin mai sanye da rigar Argentina mai dauke da sunan Messi ya shiga cikin fili a lokacin da ake tsaka da wasa a zagaye na biyu a karawar da aka yi ba ‘yan kallo sannan ya kuma samu damar yin hoton, amma dan nesa da Messi kafin jami’an tsaro su damke shi.
Mahukuntan  sun ce sun dauki lamarin da girma, domin za a iya jefa lafiyar mutane cikin hadari da kuma kaskantar da gasar ta Spaniya a idon duniya a wannan lokacin da duniya take taka tsan-tsan da lafiyar al’umma.
Mutumin ya ce ya haura katanga ne mai tsawon mita biya ya samu shiga filin wasa na Mallorca sannan ya kuma kara da cewar ya dade ya na wannan shirin, kuma tun lokacin da ya ji za a buga wasan ya tsara yadda zai je ya yi hoto da kyaftin din Argentinan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: