Wasu rahotanni daga kasar Sipaniya sun tabbatar da cewa dan wasan Barcelona, Leonel Messi, ya saka daya daga cikin gidajensa a kasuwa wanda hakan wata manuniya ce wadda take bayyana cewa ya fara shirin barin kungiyar da zarar an kammala kakar wasa ta bana.
Tuni daman aka ci gaba da samun ra’ayoyi masu cin karo da juna a tsakanin masu zawarcin shugabancin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona akan ci gaba da rike dan wasa Messi ko kuma sayar dashi a watan Janairu mai zuwa.
Wasu daga cikin masu neman shugabancin kungiyara sun bayyana cewa bai kamata kungiyar tayi sake ta rasa babban dan wasan duniyar ba ya yinda wasu suke ganin lokaci yayi da za su sayar da Messi a watan janairu wasu kuma daga cikin ‘yan takarar suke ganin zasu rabu da dan wasan idan kakar wasa ta bana ta kare.
Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German dai ta nisanta kanta da zawarcin Messi wanda ake ta rade radin cewa zai bar Barcelona a karshen kakar wasa ta bana ko kuma cikin wannan watan na Janairu kuma har yanzu ana ci gaba da alakanta dan wasan da PSG tare da Manchester City.
Manchester City dake Ingila ta sanar cewa ta hakura da zawarcin da take yiwa Messi bayan da kungiyar tayi lissafin irin kudin da zata kashe idan har ta amince zata bashi damar buga mata wasa a kaka mai zuwa.
A cikin watan Agustan daya gabata Manchester City ta so daukar Lionel Messi daga Barcelona bayan da dan wasan ya bukaci barin kungiyar sakamakon rashin jituwa da tsohon shugaban gudanarwar ta Barcelona.
Barcelona ta ci karo da cikas a kakar bara, bayan da ta kasa lashe kofi ko guda daya, bugu da kari da dukan kawo wuka da Bayern Munich ta yi mata a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League daci 8-2.
Kyaftin din tawagar na Argentina ya samu rashin jituwa da Josep Bartomeu – wanda ya ajiye aikin shugabantar Barcelona a cikin watan Oktoban shekarar data gabata wanda hakan yasa dan wasan ya bukaci barin kungiyar wadda ya fara bugawa wasa tun yana matashi.
Kwantiragin Messi zai kare a Barcelona a karshen watan Yunin shekarar nan ta 2021, wanda hakan na nufin wata kungiyar za ta iya tattaunawa da shi da nufin daukar shi daga ranar daya ga wannan watan na Janairun da muke ciki.
Dan wasan dai yana da gidaje a birnin na Barcelona kuma kamar yadda rahotanni suka tabbatar ya fara saka su a kasuwa domin sayarwa a kokarinsa na barin Barcelona wadda yake bugawa wasa kusan shekaru 17.
Manchester City ta samu damar da zata iyi amfani da ita wajen neman Messi, kyaftin din Argentina, sai dai wasu bayanai na cewa Manchester City ba za ta iya biyan Barcelona Yuro miliyan 50 ba, kudin da kungiyar za ta amince saboda halin matsi da cutar korona ta haddasa.
Tuni dai Manchester City ta haura da zawarcin dan wasan saboda yana daukar yuro miliyan 100 wanda ba karamin kudi bane a halin yanzu da kungiyoyi suka talauce sakamakon annobar cutar Korona hakan yasa dole zasu hakura da daukar dan wasan.
Sai dai a cikin a watan da ya gabata dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta PSG, Neymar, ya bayyana cewa zai iya barin kungiyar ta Faransa a kakar wasa mai zuwa idan har shugabannin kungiyar basu sayo musu Messi ba inda ya ce ba zai sake sabon kwantiragi ba har sai an cika musu wannan buri nasu.
Bugu da kari shugabannin kungiyar kwallon kafa ta PSG suna ganin idan suka dauki Messi ya koma kungiyar zasu samu damar ci gaba da rike Neymar sannan shima matashin dan wasa Mbappe zai iya zama idan har ya ga Messi ya koma kungiyar.
A kwanakin baya ne Mbappe ya sanar da shugabannin kungiyar cewa yana son barin PSG a karshen kakar wasa inda tuni kungiyoyin Juventus da Real Madrid da Liverpool suka fara nuna sha’awarsu ta ganin sun dauki Mbappe, dan Faransa.
Tuni dai aka bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar PSG ya fara shirye-shiryen tattaunawa da wakilan dan wasa Messi domin ganin ko zasu iya shawo kan dan wasan ya amince ya koma kasar Faransa da buga wasa.
Sai dai banda Manchester City, kungiyoyin Chelsea da Inter Milan da kungiyar Bayern Munchen duka sun nemi Messi sai dai a halin yanzu ana ganin PSG ce akan gaba wajen neman kaftin din na Barcelona da Argentina.