Messi Ya Sake Kafa Tarihin Zura Kwallo 50 A Shekara Daya

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kuma kyaftin kungiyar da tawagar kasar Argentina, Lionel Messi ya ci kwallonsa ta 50 a shekarar 2019 yayin da Barcelona ta casa Deportivo Alaves da ci 4-1.

Luis Suarez ne ya bayar da kwallo aka ci har uku rigis sannan ya ci ta hudu, abin da ya sa Barcelona ta dare saman teburi da tazarar kwallaye tsakaninta da Real Madrid wadda take a mataki na biyu.

Antoine Griezmann ne ya fara jefa kwallo a raga, Arturo Vidal ya kara ta biyu kafin daga baya Pere Pons ya ci wa Alaves kwallo daya sannan Messi ya ci wa Barcelona kwallo tun daga yadi na 25 sannan sai Suarez da ya ci fanareti bayan an tava kwallo da hannu.

Barcelona ta kare shekarar 2019 ba tare da tayi rashin nasara a gida ba, sannan  ta samu nasara a  wasanni 24, ta yi canjaras hudu  wanda kuma shi ne mafi tsawo da ta yi tun shekarar 2011 a filin wasa na Camp Nou dake birnin Barcelona.

Tun farko an hana kwallon da Messi ya ci, kafin daga bisani ya ci kwallonsa ta 50 ga Barcelona da Argentina a shekarar 2019 wanda kuma hakanne yasa hukumar kwallon kafa ta duniya ta zave shi a matsayin gwarzon dan kwallon duniya.

Messi ya shirya tsaf domin zama dan wasan da ya fi zira kwallaye a raga a nahiyar Turai da kwallo 34 cikin wasannin La Liga 32 da ya buga, inda ya wuce saura da kwallo biyar kawo yanzu.

Kuma sau tara kenan yana kai wa irin wannan matsayi a cikin shekara 10 da suka gabata kuma duk shekara dan wasan yana zura kwallaye sama da 40 sannan duk shekara yana iya zama gwarzon dan kwallon duniya ko kuma ya zama na biyu.

 

Exit mobile version