Messi Yafi Pele Komai A Duniya -Aguiro

Aguero

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Sergio Aguiro, ya bayyana cewa dan wasa Messi yafi tsohon dan wasan Brazil Pele komai a duniya kuma maganar yawan kwallaye da akeyi Messi shine akan gaban Pele din.

Aguiro yana wannan Magana ne a yayinda har yanzu ake takaddama tsakanin manyan gwarazan guda biyu akan wanda yafi yawan kwallaye a duniya a cikin kungiya guda daya tun bayan rahoton cewa Messi ya kamo Pele har ma ya wuce shi.

Sai dai a kwanakin baya kungiyar kwallon kafa ta Santos ta bayyana cewa har yanzu Messi bai karya tarihin na Pele ba inda tace akwai tazarar sama da kwallaye dari hudu tsakanin Pele da Messi a halin yanzu.

Amma Messi ya bayyana cewa bai damu da karya tarihin tsohon dan wasan Barzil din ba, duk da surutun da hakan ya janyo a kwanakin baya kuma zai ci gaba da zura kwallaye a raga domin ci gaba da kafa tarihi.

Messi, ya kamo tarihin da tsohon dan wasan Brazil, Pele, ya kafa na cin kwallaye 643 a kungiya daya, bayan kwallon da ya ci wa kungiyarsa ta Barcelona a wasan da ta buga da Balencia sannan ya sake zura kwallo daya wadda tasa ya zarta Pele din a wasan da suka fafata da Balladolid sai dai kawo yanzu Messi ya zura wasu kwallayen inda ko a ranar Laraba sai da ya zura kwallaye biyu a ragar Athletico Bilbao.

Sai dai a wata sanarwa da kungiyar Santos ta fitar a shafinta na Internet, kungiyar tace Pele kwallaye 1091 ya zura a raga kuma a cikin kwallayen babu wadanda ya zura a wasannin biki ko kuma na sada zumunci.

Santos ta ci gaba da cewa ana kokarin ragewa Pepe kwallaye 448 a cikin kwallayensa kuma a cikin kwallayen da ake son ragewa akwai kwallayen daya zura akan manya-manyan kungiyoyi a duniya ciki har da Inter Milan wadda take babbar kungiya a shekarar 1960.

Santos ta kara da cewa wasu daga cikin kungiyoyin da Pele ya zurawa kwallo a raga a lokacin da yake wasa akwai Riber Plate da Boca Juniors da Racing duka na kasar Argentina da Unibersidad de Chile da Real Madrid da Jubentus da Lazio da Napoli da Benfica da Anderlecht sannan sai ita kanta kungiyar da Messi yake bugawa wasa wato Barcelona inda a cikin wasanni hudu Pele ya zura musu kwallaye hudu.

Santos ta kara da cewa duka wasannin da Pele ya buga sun samu sahalewar hukumar kwallon kafa ta Brazil ko kuma ta yankin kudancin Amurka saboda haka wasannin da akace babu su a lissafi hukumomi ne suka amince ayi wasan saboda haka dole ne ayi lissafi dasu.

Messi ya buga wa Barcelona da ke Sifaniya wasanni a kakar wasa har 17 da ya yi, tun bayan fara wasansa a shekarar  2004 kuma gwarzon dan wasan Brazil ya fi kowa yawan cin kwallaye a kungiyar Santos a kakanni 19 da ya buga da kungiyar.

Har ila yau Messi na cikin manyan ‘yan wasan duniya da suke haskakawa sama da shekara 10 a jere, tare da takwaransa na Jubentus Cristiano Ronaldo wadanda cikin shekaru goma na baya suka mamaye kwallon kwafa ta hanyar lashe kowacce irin kyauta ta nuna bajinta.

Sai dai a wannan kakar Messi na fuskantar koma baya na rashin kokarin kungiyarsa ta Barcelona wadanda wasu ke dora alhakin hakan a kan shi duk da cewa a kwanakin baya ya bayyana cewa yana son barin kungiyar.

Exit mobile version