Mijin Sufetar ‘Yan Sandan Da Ta Mutu Ya Zargi Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Umahiya Da Sakaci

cibiyar

Daga KALU EZIYI,

Mijin wata marigayiyar sufeton ‘yan sanda, Isabella Ntiasagwe wanda ta mutu a ranar Asabar da ta gabata a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), Umuahia ya zargi cibiyar kula da lafiya da yin sakaci wajen ceton rayuwarta.

Da yake bayyana kaduwarsa game da lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai a babban birnin jihar Abia, Okalekan Saliu ya ce an yi wa matar tiyata ne a ranar Alhamis din da ta gabata kuma ta fitoa natse bayan haka ba tare da wata damuwa ba.

“Amma bayan ‘yan awanni kadan da fitar ta daga dakin tiyata sai ta fara zubar da jini sosai, hakan ta sa aka kara mata jini laida tara, amma duk da hakan abin yi wani tasiri ba har sai da ta mutu.”

Saliu ya lura cewa yana da kyakkyawan dalili cewa lokacin da yanayinta ya kara ta’azzara, sai ma’aikatan jinya da ke bakin aiki suka yi ta kira ga likita don ya zo ya duba ta, amma ya kasa zuwa.

Da yake bayanin cewa ya yi aure kimanin shekaru shida da matar tasa haifaffiyar jihar Imo, ya kara da cewa ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na yankin Umuahia.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PRO), Darlington Madubuko ya ce zai nemi sanin ko an kai rahoton lamarin gare su, inda ya ce kai rahoton ga ‘yan sanda abu ne da ya dace.

Sai dai ya ce irin wannan ya dace ne a rika sanar da wadda ya dace cibiyar tun da tana da shugaban da ke kula da harkokinta, kana ya yi Allah wadai da halayen mutanen da suke fusata tare da ke garzayawa zuwa ga manema labarai don yin korafi ba tare da fara sanar da wanda ake zargi da aikata laifin ba.

 

Exit mobile version