Connect with us

WASANNI

Mikel Obi Zai Iya Buga Wasan Yau Da Argentina

Published

on

Tawagar Likitocin Super Eagles da ke wakiltar Nijeriya a gasar cin kofin duniya a Rasha na aiki ba-dare-ba-rana donin ganin Mikel Obi ya samu cikakkiyar lafiyar buga wasan da Nijeriya za ta yi da Argentina a yau Talata.
Binciken likitocin ya nuna cewa, dan wasan ya samu rauni a wuyar hannunsa a dai dai lokacin da ake dab da tashi wasan da Nijeriya ta casa Iceland da ci 2-0 a ranar jumm’ar da ta gabata.
Koda dai Kocin Super Eagles, Gernot Rohr na kallon runin a matsayin karami wanda kuma ba zai hana Obi buga wasan da Argentina ba.
Rohr ya kuma bukaci ‘yan wasan nasa da su rika dukan kwallo da zaran sun hangi wata kafa a dab da ragar Argentina.
Rohr ya ce, wasan na yau ba zai kasance mai sauki ba, kuma za su yi fafatawar ce da burin samun nasara amma ba canjaras ba kamar yadda wasu ke fata.
Masu sharhi akan harkokin wasanni na kallon wasan a matsayin mai zafi kwarai, lura da cewa Argentina na neman nasara ruwa a jallo don tsallakawa matakin gaba, yayin da ita ma Nijeriya za ta yi kokarin samun karin maki domin kaiwa mataki na gaba na kasashe 16.
Advertisement

labarai