Miliyoyin Jama’a Za Su Koma Jamiyyar APC, Cewar Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, miliyoyin jama’a daga sassan kasar nan zasu koma Jamiyyar APC nan gaba kadan, Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wata wasika da  ya aika wa tsohon sanata Basheer Mohammed wanda ya fice daga  jamiyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Wasikar wanda aka rubutata a ranar 25 ga watan January 2018, Shugaba Buhari ya yi bayani kamar haka ni ina farin ciki da samun wasikar ka ta hanyar sanar da ni domin shigowa jamiyyar mu ta APC, ‘ina da yakinin zaka jawo dubun mutane zuwa jamiyyar nan gaba sakamakon ficewarka daga jam’iyyar PDP’ inji Shugaban.

Shugaba Buhari, ya kara da cewa, ina mai farin cikin tarbarka a fadar shugaban kasa a nan gaba.  A makon da ya gabata ne  aka bude ofishin gangamin takarar Shugaba Buhari a Ibadan babban birnin jihar Oyo, wannan alamun cewa, Buhari zai sake tsayawa takara a zaben 2019.

 

Exit mobile version