Minista Idris Ya Ƙaddamar Da Ƙungiyar Kakakin Labarai 
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Minista Idris Ya Ƙaddamar Da Ƙungiyar Kakakin Labarai 

bySulaiman
2 years ago
Minista

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaddamar da Ƙungiyar Kakakin Labarai (spokesmen), inda ya buƙace su da su yi amfani da ilimi, gogewa, da guraben da ake da su a ƙungiyar.

Ministan ya yi magana ne a ranar Alhamis a gaban tawaga daga Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ƙarƙashin jagorancin Farfesa Emmanuel Dandaura, muƙaddashin shugaban cibiyar, wadda ta kai masa ziyara a ofishin sa a Abuja.

  • Minista Yaɗa Labarai Ya Nemi Masu Zanen Gine-gine Su Farfaɗo Da Tarihin Ginin  Nijeriya
  • Sojoji A Jihar Katsina Sun Fatattaki ‘Yan Bindiga Tare Da Kubutar Da Mutane

Ministan ya bayyana rawar da kakakin labarai su ke takawa a matsayin masu tace labarai a kafofin su daban-daban, “ko a cikin gwamnati, sashi masu zaman kan su, sashen cigaba, ko kuma sashen sa kai, masu magana da yawun su na da muhimmiyar rawa wajen ƙwato martabar ƙungiyoyin su da al’umma a cikin dogon lokaci.”

Ya ce hakan ne ya sa ma’aikatar sa ta haɗa kai da cibiyar wajen shirya wannan taro.

Idris ya kuma buƙaci kakakin labaran da su tuna cewa domin samun nasara a muhimman ayyukan da aka ba su, dole ne su kasance su na da cikakkun kayan aiki da horaswa da kyawawan ɗabi’u da za su riƙa nuna ƙungiyoyin su da ƙasar su da kyau.

Ya buƙace su da su ware ranakun 25 – 28 ga Maris, 2024, a kalandar su domin gudanar da taron.

Bugu da ƙari, ya yaba wa wannan shiri kuma ya ce ya zo a daidai lokacin da ya dace da gwamnati za ta inganta Yarjejeniyar Ƙimar Ƙasa.

Ministan ya ba da tabbacin cewa kakakin labarai za su ɗauki saƙon, su yi amfani da shi, sannan su yaɗa shi ta hanyar ƙungiyar su.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Next Post
Afcon

AFCON 2023: Yadda Abubuwan Mamaki Ke Faruwa A Gasar

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version