Daga Nasir S. Gwangwazo,
Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta samarwa da nakasassun dake Nijeriya hanyoyin da za su rika bi a dukkan gine-gine da wurare na gwamnati irin su filayen jirgin sama, tashoshin jirgin kasa da na mota da makarantu.
Ministar ta yi kiran ne a lokacin da ta gabatar da Shugaba da membobi da Babban Sakataren Cibiyar Nakasassu ta Kasa ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Hajiya Sadiya ta gode wa Shugaban Kasa saboda yadda ya amsa kiran nakasassun ta hanyar rattaba hannu kan Dokar Kula da Nakasassu ta Kasa sannan ya kafa Hukumar Nakasassu ta Kasa. Amma ta yi nuni da cewa mutane masu nakasa a kasar nan an ware su daga cin moriyar wasu ababe na more rayuwa.
Ta ce, “Akwai bukatar a fito da hanyoyin da za su rage rainin da ake yi wa mutane masu nakasa ta hanyar fito da babban gangamin fadakar da jama’a, tare da cire duk wasu nau’o’i na nuna wariya da kuma inganta hanyoyin su na samun abinci.
“Akwai bukatar a samu cikakkun bayanai game da nakasassu, sannan bada satifiket din nakasassu ya na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa su na cin moriyar wannan hukumar don a kauce wa cutar da wasu za su iya yi a aikin kyautatawar da gwamnati za ta rika yi.”
Har ila yau ministar ta bayyana cewa ta bai wa nakasassu kayayyakin agaji don tabbatar da cewa su ma sun amfana da ayyukan da ma’aikatar ta ke yi da kuma dukkan shirye-shiryen inganta rayuwa.
Ta ce, “A yau dubban nakasassu an taimaka masu kai-tsaye ta hanyar shirye-shiryen mu daban-daban.”
Hajiya Sadiya ta yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da bada goyon baya don tabbatar da cewa an kyautata rayuwar dukkan nakasassu da ke Nijeriya.
A jawabin da ya mayar, Shugaba Muhammadu Buhari ya kalubalanci Hukumar Nakasassu ta Kasa da ta yi aikin ta sosai wajen ganin an cimma kudirin gwamnati na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin fatara da yunwa.
Ya ce, “Ba a yi kuskure ba wajen nada ku da aka yi domin kuwa dukkan ku an zabo ku ne bayan an yi nazari sosai kan halayen ku da kuma gudunmawar da ku ke bayarwa ga al’umma da kuma nakasassun da ke Nijeriya.
Shugaban ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bada goyon baya ga duk wasu yarjejeniyoyi da ke kare hakkin mutane masu nakasa.
Ya ce, “Nijeriya ta na cikin kasashen da su ka rattaba hannu kan Kudirin Majalisar Dinkin Duniya kan Mutane Masu Nakasa wadda ke neman ganin an kare hakkin nakasassu a dukkan wani shiri na kawo cigaba a duk duniya.
“A karkashin shugabanci na, gwamnati za ta ci gaba da goyon bayan duk wasu yarjejeniyoyi da aka yi na duniya da yanki ko sashen kasa da kasa wadanda ke neman inganta rayuwar ‘yan’uwan mu masu bukatu na musamman.”
Tun da fari dai sai da Majalisar Dattawa ta gama aikin tantance tare da amincewa da nadin Hon. Dakta Husseini Hassan Kangiwa daga yankin Arewa Maso Yamma a matsayin Shugaban Hukumar Nakasassu ta Kasa kamar yadda Sashe na 32(3) da na 40(1) na Dokar Hana Wariya Ga Nakasassu ta 2019 ta tanadar.
Sauran membobin hukumar su ne Mrs. Esther Andrew Anwu (Memba daga Arewa ta Tsakiya), Malam Abba Audu (Memba daga Arewa ta Gabas), Malama Amina Rahma Audu (Memba daga Arewa ta Yamma), Mista Jaja Oparaku (Memba daga Kudu Maso Gabas), Ms. Philomena I Konwea (Memba daga Kudu Maso Kudu) da Mista Omopariola Busuyi (Memba daga Kudu Maso Yamma). Sai kuma Mista James Dabid Lalu a matsayin Babban Sakatare daga Arewa ta Tsakiya.