Nasir S Gwangwazo" />

Minista Sadiya Ta Karyata Zargin Cin Hanci Da Rashin Alkibla

Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta karyata wani labari da aka bayar inda aka ce wai akwai cin hanci da rashawa da kuma rashin alkibla a shirin ma’aikatar ta na raba agajin kudi ga mata marasa galihu.

A cikin wata sanarwa da ta rattaba wa hannu a cikin wannan makon, ministar ta ce labarin da jaridar Thisday ta buga a ranar Lahadi, 24 ga Janairu, 2021 inda aka yi wannan ikirarin duk zuki-ta-malle ce da rashin fahimtar hakikanin manufar shirin.
Ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fito da shirin na ‘Household Uplifting Programme-Conditional Cash Transfer (HUP-CCT)’ a shekarar 2016 ne tare da hadin gwiwar Bankin Duniya da nufin samar da kariya daga fatara ga mabukata a Nijeriya.
“Hakan ya yi daidai da shirin gwamnatin Shugaba Buhari na inganta rayuwa tare da yakar fatara da yunwa a cikin al’umma,” inji ta.
Hajiya Sadiya ta ce a shirin ana biyan kudi N5,000 ne ga gidajen fakirai wadanda yawanci a yankunan karkara su ke.
Mijistar ta bayyana cewa shirin ya na da wasu manufofi da su ka hada da:
1. Inganta abincin da ake ci a cikin gidaje tare da gyara yanayin tattalin arzikin jama’a;
2. Kara yawan hanyoyin inganta kiwon lafiya da abinci;
3. Inganta shigar yara makaranta da ci gaba da karatun su;
4. Inganta kiwon lafiya a tsakanin al’umma;
5. Inganta hanyoyin samun kudi da kayan ayyukan yau da kullum da kuma inganta tattalin arzikin iyali da rage musu fatara.
6. Rungumar masu cin moriyar shirin tare da kuma hanyoyin samun abincin su.
Ministar ta ce gaba daya ma dai shi wannan shiri wani bangare ne na kudirin gwamnati na rage fatara a cikin al’umma a Nijeriya.
Yayin da ta ke bada jadawalin nasarar da shirin ya samu, Hajiya Sadiya ta ce ya zuwa watan Disamba na 2020, an gudanar da shirin a jihohi 33 na kasar nan har da Yankin Babban Birnin Tarayya. Sannan an samu jimillar mutum 1,414,983 da su ka ci moriyar shirin da gidaje 7,068,629 da aka shigar cikin shirin, wanda ya shafi Kananan Hukumomi 487, unguwannin mazabu 4,716 da kuma kauyuka 37,628.
A cewar ta, shirin na da burin ya isa kowace jiha ya zuwa watan Maris, 2021.
Ta ce, “Akasin ikirarin da aka yi na cewar wai shirin bai da tsarin gudanarwa, a gaskiya wannan shiri ya na da kyakkyawan tsarin aiwatarwa tare da hanyoyi a rubuce a komfuta kan yadda ake rubuta sunayen duk wadanda su ke cin moriyar sa, wanda ya ginu a kan gidajen fakirai ko marasa galihu wadanda ake samo bayanan su daga Rajistar Jama’ar Kasa, wato ‘National Social Register’.
Sadiya ta ce, “Ana samun irin wadannan mutane ne ta hanyar tsarin bincike da tambayar jama’a wanda sashen jami’ai masu kula da kowace jiha da mu ke da su, wato ‘State Operating and Coordinating Units (SOCU)’ a karkashin kulawar ofishin mu mai kula da binciko hanyoyin yaki da fatara na kasa, wato ‘National Social Safety Net Co-ordination Office’ (NASSCO) su ke yi.
“Hanyar binciken yanayin al’umma da mu ke da shi (CBT) shi ne mu ke amfani da shi wajen gano wadanda ya dace su ci moriyar shirin.”
Ministar ta kara da cewa ya zama wajibi ta yi karin wasu bayanai ga jama’a don su fahimta sosai. Bayanan su ne:
1. Ana samun bayanan gidajen fakirai ne a matakin jiha, kuma Ma’aikatar Tsare-tsare ta kowace jiha ce ke da sunayen. Ana samun wannan bayanin ne daga gidan yanar shirin kare jama’a daga fatara na kasa, ‘National Social Safety Net Project’ (NASSP), wato www.nassp.gov.ng;
2. Dukkan shirye-shirye guda uku na bada tallafi da ake gudanarwa su na cikin tsarin kasafin kudi da aka yi ne, kuma ana aiki da su ne ta hanyar komfuta.
i. Akwai wata ma’adanar bayanai mai suna ‘Rapid Transfer Register (RRR)’ wadda aka tanadar a karkashin Shirin Inganta Tattalin Arzikin Kasa, wato ‘Economic Sustainability Plan’ (ESP).
ii. Akwai shirin bada tallafin kudi, wato ‘Conditional Cash Transfer’ (CCT) wanda kudin da aka karbo daga asusun Abacha ne da kuma rancen Bankin Duniya ake amfani da su.
iii. Akwai shirin bada tallafin kudi ga matan karkara, wato ‘Cash Grant to Rural Women’ (CGRW), inda ake yin biya guda daya kacal, shi kuma an samar da shi ne a cikin Dokar Kasafin Kudi ta shekarar 2020.
3. Akwai biyan kudi ta hanyar tiransifa da ake yi ta yadda har ake inganta wurin da ake aikin a ko’ina, kuma an lura da cewa al’ummar da ke amfana da shirin na CCT su ne su ka fi kowa fatara kuma yawanci su na zaune ne a yankunan karkara inda babu banki ko wayar hannu.
4. A farkon fara shirin a cikin Satumba 2016, an rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Tarayya da dukkan jihohi. Wasu jihohin sun rungumi shirin nan take yayin da wasu su ka zo daga baya. Wannan ya sanya wasu jihohin sun yi wa sauran nisa wajen samar da sunayen gidajen fakirai daga Rajistar Jama’a ta Jiha.
5. Shigo da masu biyan kudi, wato ‘Payment Service Providers’ (PSPs), an yi shi ne ta hanyar tsarin shiga neman kwangila na kasa (NCB) wanda Bankin Duniya ya kawo. Wannan ne ya sa ake ganin babu wani kumbiya-kumbiya a lamarin.
6. Shirin CCT ya samar da inganta karfin samu, koyarwa da bin diddigi ga masu cin moriyar sa a kan batutuwa masu yawa da su ka hada da kiwon lafiya, ilimin yara mata, ajiya, da sauran su. Kafa kungiyoyin gama kai da ajiya abubuwa ne na sa kai, ba tilas ba, kuma su masu cin moriyar ne ke gudanar da abin su ba tare da sa hannun hukuma ba.
A yanzu, an samar da Rajistar Jama’a ta Jiha a kowace jiha, a yayin da ake aiwatar da shirin na CCT a dukkan jihohi 36 in ban da Borno, Ebonyi da Ogun inda ba a soma biya ba.
Ministar ta jinjina wa kan ta da cewa, “An samu dimbin sakonnin yabo da godiya daga gwamnatocin jihohi da dama a game da shirin, akwai kuma dimbin labaran da mutane ke bayarwa kan yadda shirin ya yi tasiri a rayuwar wadanda ke cin moriyar sa da kuma yadda ya taimaki al’ummomin fakirai ‘yan Nijeriya su ma.”
A karshe, Hajiya Sadiya ta ce: “Burin Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ne ta tabbatar da cewa an aiwatar da shirin gwamnati na yaki da fatara da yunwa kamar yadda ya kamata, saboda ya tafi kafada da kafada da shirin mai girma Shugaban Kasa na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin fatara da yunwa kafin shekara ta 2030.”

Exit mobile version