Connect with us

RAHOTANNI

Minista Shari’a  Ya Bada Tallafin Kayan Abinci Ga  Jama’ar  Kebbi  

Published

on

A jiya ne ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami ya bada tallafin kayan abincin ga jama’ar jihar kebbi ta hannun wata cibiyar tallafawa al’ummar a jihar  da Ministan ya kafa don tallafawa al’ummar a koda yaushe mai suna “Khadimiyya Foundation”  ta raba Tirelolin kayan abincin ga Jama’a a jihar ta kebbi don tausaya wa ga irin radadin da kuma halin da Jama’a suke fuskanta kan  matsalar cutar coronabirus da kuma irin bukatar da ke akwai kan watan Azumin Ramadan da muki ciki.

 

Abincin da cibiyar Khadimiyya Foundation ta raba amadadin ministan shari’a Abubakar Malami sun hada da Buhu Dubu 2600 na Shinkafa, Buhu Dubu 1,000 .00 na hatsi , Buhu Dubu 1,000.00 na Suga, Katon dari 300 na Sufageti da kuma jarka Dubu 1,000.00 na man dafa abinci da sauransu.

 

Haka kuma wadanda zasu cigajiyar tallafin na kayan abinci da ministan shari’a Abubakar Malami ya bayar domin a raba su ne marayu, Nakassasu, zaurawa, Talakawa da kuma Shuwagabannin addinai sai kuma magidanta wadanda mabukata ne da kuma sauran wasu kungiyoyin masu zaman kansu da ke taimawa al’ummar.

 

Shugaban Kungiyar Khadimiyya Foundation  Alhaji Malami Abdulkadir ya bayyana wa manema labaru cewa ” Domin tabbatar da ce wannan tallafin kayan abinci da ministan shari’a Abubakar Malami ya kawo  ya kai ga wadanda a mabukata mun kafa Kwamitin amintatu a karkashin jagorancin Bello Muhammad Nasarawa don raba wannan tallafin ga Jama’ar da ministan ya bada umurnin tallafa musu a duk fadin jihar ta Kebbi” ,Inji shugaban kungiyar Khadimiyya.

 

Haka kuma ya kara da cewar ” zamu tabbatar da umurnin da ministan shari’a ya bayar an yi aiki dashi wuri ganin cewar mabukatan sun cigajiyar tallafin nashi. Kayan tallafin dai na abinci da ministan  shari’a na kasa ya kawo don rabawa jama’a an raba su ne a bakin harabar Babban ofishin kungiyar kwadago da aka fi sani da (Labour House) da ke  Birnin-Kebbi a jiya.

 

Ya cigaba da cewar wannan tallafin kayan abincin domin a rage yawan radadin da Jama’a ke fama dashi na yinwa da kuma  halin da aka shiga na matsalar cutar coronabirus da a ke fama da ita a duk fadin kasar Najeriya baki daya”, lnji shi”.Shima a nashi jawabi yayin da suke raba kayan abincin, shugaban Kwamitin rabon Bello Muhammad Nasarawa ya bada tabbatacin raba kayan abincin ga dukkan jama’ar da ministan ya ambata don tabbatar da an tallafa musu a duk fadin jihar ta Kebbi insha Allah.

 

Haka yana matukar godiya ta musamman ga maigirma ministan shari’a Abubakar Malami kan irin wannan sadaukar da kansa da yake yi wurin ganin ya tallawa jama’ar jihar ta Kebbi . Saboda hakan muna godiya kwarai da gaske.

 

Bugu da kari yayi kira ga masu hannu da shunni da kuma masu rike da mukaman gwamnatin jihar da na tarayya da suyi koyi da ministan shari’a wurin bada tallafin ga Jama’arsu don taimakawa ga irin kokarin da gwamnatin keyi wurin ganin cewar jama’arta basu shiga cikin ma wuyacin hali ba.

 

Daga karshe yayi kira ga al’ummar jihar ta Kebbi da su tabbatar da sun bi ka’idodin da kuma shawarwarin da jami’an kiyon lafiya  da kuma su kansu Kwamitin da gwamnatin jihar Kebbi ta kafa kan coronabirus don kariya ga kamuwa da cutar ta corona da kuma basu cikaken goyon baya don gudanar da ayyukkansu cikin sauki .
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: