Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home LABARAI

Minista Ta Nemi Samun Karin Mata A Bangaren Albarkatun Man Fetur

by Sulaiman Ibrahim
March 28, 2021
in LABARAI
2 min read
Minista Ta Nemi Samun Karin Mata A Bangaren Albarkatun Man Fetur
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Bello Hamza, Abuja

A ranar Juma’a ne Ministar harkokin mata, Mrs Pauline Tallen, ta bayyana bukatar neman karin mata a bangaren ayyukan albakatun man fetur da iskar gas na tattalin arzikin kasar nan.
Bayanin haka na kunshe ne a takardar manema labarai da jami’in yada labarai na ma’aikatar, Mr Shehu Maikai ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a Abuja.
Maikai ya bayyana cewa, Minista Tallen ta yi kiran ne a yayin da mambobin kungiyar mata masu aiki a bangaren albakatun man fetur da iskar gas ta kasa suka kai mata ziyara a ofishinta da ke Abuja.
Ta ce, maza sun mamaye bangaren na tsawon lokaci kuma ya kamata a halin yanzu a samu mata masu fafatawa a bangaren suma su bayar da gudumwarsu a bangaren na tattalin arzikin kasar.
Ta kuma ce, a kasar da kusan rabin al’ummar mata ne babu dalilin da zai sanya a ce kashi 15 na mata kawai ne cikin ma’aikata a bangren harkar man fetur da iskar gas na kasar.”
Daga na ta kuma kara da cewa, lokaci ya yi da matan Nijeriya za su shiga a dama da su a dukkan bangarorin rayuwar al’umma, kuma wannan gwamnatin za ta bayar da gudummawar ganin hakan ya faru, don haka ne za a tabbatar da daga darajar mata su kuma bayar da nasu gudummawar a kokarin farfado da tattalin arzikin kasar nan.
Ministan ta kuma yaba wa ‘yan kungiyar a kan yadda suke kokarin ganin an samu karin mata a bangaren harkar man fetur da iskar gas.
Ta kuma yaba musu akan yadda suka shiga fafutukar ganin yara mata sun shiga makaranta da kuma kokarin samar da tsaftaccen ruwan sha ga al’umma.
A nata jawabin, shugabar kungiyar, Dr Oladunmi Owo, ta ce, sun kawo ziyara ne don neman goyon bayan ma’aikatan a harkokinsu na bunkasa rayuwar mata a Nijeriya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, Attahiru, Ya Karbi Allurar Rigakafin Korona

Next Post

Jami’ar Ahmadu Bello Ta Samu Tallafin Naira Biliyan 1 Daga Gidauniyar ‘Africa Initiative’

RelatedPosts

Sace Daliban Jami’a A Kaduna: Yadda ‘Yan Bindiga Suka Shammaci Jami’an Tsaro

Sace Daliban Jami’a A Kaduna: Yadda ‘Yan Bindiga Suka Shammaci Jami’an Tsaro

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Daga Abubakar Abba, Kaduna A daren ranar Talata da dare...

Gwamnan Gombe Ya Nuna Takaicinsa Kan Masu Gina Gidajen Mai A Unguwanni

Gwamnan Gombe Ya Nuna Takaicinsa Kan Masu Gina Gidajen Mai A Unguwanni

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Gombe Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu...

Gwamnatin Kano

Kungiyar ‘Yan Fansho Ta kasa Ta Karrama Gwamna Ganduje

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

kungiyar 'Yan Fansho ta kasa ta bai wa Gwamnan Jihar...

Next Post
Jami’ar Ahmadu Bello Ta Samu Tallafin Naira Biliyan 1 Daga Gidauniyar ‘Africa Initiative’

Jami'ar Ahmadu Bello Ta Samu Tallafin Naira Biliyan 1 Daga Gidauniyar ‘Africa Initiative’

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version