Daga Bello Hamza, Abuja
Ministar Jinkai da bayar da agajin gaggawa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta umarci hukumar NEMA da ta kai agajin gaggawa ga ‘yan kasuwar da suka yi asara sakamakon gobarar da ta auku a kasuwanin garuruwan Katsina da na Zamfara.
Minista Sadiya Farouk ta bayyana haka ne a sanarwa da ta raba wa manema labarai ta hannun jami’ar watsa labaran ta Mrs Nneka Anibeze a Abuja ranar Talata, ta kuma nuna alhininta akan gobarar da ta auku.
“Na umarci hukumar ta bayar da tallafin da suka kamata ta kuma sa ido akan yadda al’amurra ke tafiya a jihohin,” inji ta.
Miniatar da kuma ce, ta yi takaici abin da ya faru, musamman yadda ya auku a daidai lokacin da Nijeriya ke farfadowa daga fuskantar annobar cutar korona.
“A madadin ma’aikatar mu, muna mika jaje ga al’ummar jihar Katsina da Zamfara, musamman ‘yan kasuwar da gobara ta rutsa da dukiyoyinsu.
“Yayin da ake cigaba da tattara alkalummar irin barnar da ya auku a gobarar, za mu cigaba da bayar da irin taimakon da suka kamata don rage musu radadin matsalar da za su shiga.