Abubakar Abba" />

Minista Ya Bukaci Manoma Su Karbi Ragamar Kula Da Shiriye-Shiryen Noman Rani

Jihar Ondo

An shwarci manoma da kuma kungiyar masu amfani da Ruwa ta kasa (WUA) dasu karbi ci gaba da kula da tsarin tafiyar da ragamar noman rani dake kasar nan.

Ministan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa Alhaji Suleiman Adamu ne ya yi wannan kiran kwanan baya a taron wayar da kai na kwana biyu kan dabarun karfafawa da kuma kula da shirye-shiryen noman rani na dake a kasar nan.
A cewar Ministan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa Alhaji Suleiman Adamu, hakan zai taimaka matuka wajen kula dasu yadda ya dace wajen samar da isasshen abinci a kasar nan da kuma rage asara.
Ministan Ma’aikatar er Albarkatun Ruwa Alhaji Suleiman Adamu ya kara da cewa, yana da mahimmanci daukacin masu ruwa da tsaki su rungumi shiga cikin tsarin kula da noman rani na (PIM) wanda aka sani shine mafita wajen magance kalubalen.
Alhaji Suleiman Adamu wanda Mista Tauheed Amusan da ya fito daga Ma’aikatar ta Albarkatun Ruwa ya wakilce shi a wurin taron ya kara da cewa, tsarin Gwamnatin Tarayya na na bunkasa fannin noman rani zai taimaka matuka wajen samar da abinci da kuma samar da ayyukan yi ga yan kasar nan.
A cewar Ministan Ma’aikatar er Albarkatun Ruwa Alhaji Suleiman Adamu ta hanyar wannan tsarin na PIM, manoma da kuma masu kula da magudanai dake kasar nan, dasu karbi ragamar ci gaba da shirin noman na rani yadda zasu samar da kudin shiga.
Alhaji Suleiman Adamu ya kuma bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya maici ta na son taga ana kara habaka yadda ake samar da abinci a daukacin fadin kasar nan, inda hakan ya sanya ta fitar da manhaja don samun cin nasarar hakan a kasar nan da kuma kara yawan wajajen yin noman rani da suka kai a kalla daga kadada 150,000 zuwa kadada 170,000.
A cewar Ministan Ma’aikatar er Albarkatun Ruwa Alhaji Suleiman, Adamu, tsarin noman rani da kula da magunai da aka kirkiro a shekarar 2016, nan ma ya yi kira da a karfafa tsarin zuwa kashi uku don a kalla wuraren yin noman rani da suka kai yawan 500,000 nan da shekarar 2030.
Alhaji Suleiman ya kuma bayyana cewa, jaddawalin da ake aiwatar dashi a gefen tekuna da kuma hukumomin da sume wanzar dashi kamar Bankin Duniya a karkashin shirin su na noman rani.
Ministan Ma’aikatar er Albarkatun Ruwa Alhaji Suleiman Adamu ya kuma nuna jin dadnsa kan yadda aka samar da tsarin na noman rani a kasar nan, sai dai ya yi nuni da cewa, kalubalen da ake fuskanta ya hada da, yadda ake samun karuwar alummar kasar nan, inda ya nuni da cewa, akwai bukatar a magance kalubalen da ake fuskanta a fannin na noman rani.
A nasa jawabin tunda farko, Daraktan noman rani da kula da magudann ruwa na Ma’aikatar ta Albarkatun Ruwa ta Tarayya Dakta Elijah Aderibigbe ya ce, tsarin na PIM ya bayar da dama don sanya masu ruwa da tsaki don gano ayyukan da za’a wanzar din a daukaka yadda za’a ci gaba da gudanar dashi.
A cewar Daraktan noman rani da kula da magudann ruwa na Ma’aikatar ta Albarkatun Ruwa ta Tarayya Dakta Elijah Aderibigbe ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a samar da wani tsari kamar irin na PIM, unda hakan zai baiwa masu ruwa da tsaki a fannin sanin yancin su da kuma rawar da za su taka akan tsarin.
Daraktan noman rani da kula da magudann ruwa na Ma’aikatar ta Albarkatun Ruwa ta Tarayya Dakta Elijah Aderibigbe, ya kara da cewa, akwai bukatar a sake yin tunani akan hakan, musamman ganin yadda Gwamnatin Tarayya take baiwa noman rani a daukacin fadin kasar nan fifiko don a samu cin nasarar aikin noman rani.
A cewar Daraktan noman rani da kula da magudann ruwa na Ma’aikatar ta Albarkatun Ruwa ta Tarayya Dakta Elijah Aderibigbe, manoman dake da sha’awa dole ne su dinga yawan tattaunawa da sauran su, inda ya kara da cewa, hakan zai bayar da dama wajen kula da shirin yadda ya dace.
Ya yi nuni da cewa, don kula da yadda wuraren noman rani suke, akwai bukatar a dinga yawan bibiyar su da kuma sanya ido ga wadanda suke da ra’ayin, musamman don a wanzar dashi a cikin nasara.
Shi ma a nasa jawabin a wurin taron, wani kwarre a fannin ban ruwa da kula da magudanai Alhaji Inuwa Musa ya yi kira da a gaggauta gabatar da kudurin yadda zai zama doka, inda ya kara da cewa, hakan zai ttaimaka matuka.
A karshe kwarren a fannin ban ruwa da kula da magudanai Alhaji Inuwa Musa tsarin yana da matukar mahimmanci a fannin na noman rani a kasar nan

Exit mobile version