Minista Ya Sha Da Kyar A Wurin Taron APC

Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, a ranar Lahadi da yamma ne ya tsallake rijiya da baya, yayin da wasu ‘yan banga suka farmaki wani taron Jam’iyyar APC a wani Otel da ke Awka, ta Jihar Anambra.

An ce su na taron ne domin samar da fahimtar juna kan sakamakon zaben mazabun Jam’iyyar da aka yi ranar Asabar.

Kawai sai aka ji harbe-harbe sun ruda wajen taron, inda nan take aka yi kokarin fidda Ngige daga wajan. Sai kuma jami’an tsaro suka mayar da martanin watsa masu harbe-harben da suka so afka masa, ta yin harbi a sama.

Wadanda suka kawo harin su na zargin Ministan yana kokarin canza sakamakon zaben mazabun ne zuwa yanda shi yake so.

Wani wakilin kwamitin shirya taron na Jihar mai suna, Ali, an ce shi bai yi sa’an gujewa maharan ba, domin kuwa sun lakada ma shi dan karen duka suka kuma yi ma shi tsirara, suna ma su zargin yana daga cikin wadanda Ngigen ya yi haya domin su canza masa sakamakon zaben.

Dan takarar gwamna a Jam’iyyar APC din a Jihar Anambra, a zaben 18 ga watan Nuwamba 2017 , Dakta Tony Nwoye, ya fito karara yana zargin Ngige a wajen taron da cewa, yana kokarin mayar da Jam’iyyar mallakin sa ne a Jihar.

A wajen taron, Nwoye, ya shaidawa Ngige cewa, yana riya cewa, an yi taron Jam’iyyar na Jihar a ranar Asabar, alhalin kuma ba wani taron da aka yi.

Nwoye ya ce, ya jima yana kokarin kaucewa yin magana kan irin karfin ikon da Ngege yake da shi a al’amuran Jam’iyyar a Jihar, don gudun kar a ce yana jin zafin faduwar zaben da ya yi ne a karkashin Jam’iyyar.

Ya ce, “Wasun ku a nan kun yi mani gabar ‘yar gida a lokacin zaben, amma ni jin dadi na shi ne, yanda ban ci zaben ba, kuma ba ku ci naku zaben ba.

 

 

Exit mobile version